Mun ga mutuwa tsirararta – Wadanda suka tsira daga harim bam a Maiduguri
A Talatar da ta gabata ce wasu mata ’yan kunar bakin wake suka tayar da tagwayen boma-bomai a babbar kasuwar Maiduguri (Monday Market), Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da Mutane 30.Wani day a shaida al’amarin, Abubakar Ibrahim, ya fada wa Aminiya cewa: “Ina tsaye, na gama cinikin takalmi ke nan sai […]
A Talatar da ta gabata ce wasu mata ’yan kunar bakin wake suka tayar da tagwayen boma-bomai a babbar kasuwar Maiduguri (Monday Market), Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da Mutane 30.
Wani day a shaida al’amarin, Abubakar Ibrahim, ya fada wa Aminiya cewa: “Ina tsaye, na gama cinikin takalmi ke nan sai na ji karar bom din, kodayake dai akwai tazara tsaknina da wajen da bom din ya tashi, to amma ina hangen macen da ta zo da bom din kuma a gaskiya mun tsira da kyar ni da abokina. Amma na ga yadda naman mutane ya yi daga-daga, a gaskiya na ga abin da ban taba gani ba kuma ban taba tsammanin zan gani ba, domin na ga mutuwa tsirararta. To Allah Ya sa ina daya daga cikin wadanda muka kai taimakon gaggawa ga mutanen da bom na farko ya tashi da su.
Shi ma Malam Goni yana daya daga cikin ’yan kasuwar da bom din ya tashi a kan idonsa kuma ya fadi cewa: “Ni kam na tsira da kyar. Tun daga tashin bom na farko har na biyun, na makale ne a cikin shagona da yake babu wata tazara mai nisa a tsakanina da inda ’yan kunar bakin waken suka yi wannan mummunar ta’asar, to amma sai dai a lokacin da bom na farko ya tashi ina waje ne, na kuma rasa inda nake don na dauka abin ya hada da ni. Ni dai kawi na gan ni a cikin shagona ne, ban san yadda na yi na shiga shagon ba.” Ya ce tare da shi aka fita wajen agajin kwashe gawarwaki da wadanda suka samu raunuka.
Shi kuwa Malam Ali Bukar, ya ce yana cikin tsakiyar filin da bom din ya tashi, na farko da na biyu. Kamar dai yadda yake cewa: “A lokacin da bom na farko ya tashi da matar, na runtuma don kai gudunmuwata, na kuma ceto wasu mutanen da Allah Ya ba ni ikon cetowa. A hanyata ta komawa wurin ne bom na biyu ya sake tashi, wato kafin in sake shiga wurin ke nan a saboda haka zan iya cewa na tsallake rijiya da baya; domin kuwa da na koma wurin to da abin ya hada da ni, domin a lokacin da na biyu ya tashi, ya hada ne da duk mutanen da suka kai gudunmuwarsu ga wadanda harin farko ya rutsa da su. A gaskiya na yi karfin hali na shiga wurin na kuma ceto jama’a da dama wadanda abin ya rutsa da su da kuma wanda bai rutsa da su ba amma suna bukatar taimako.”