Mun ga tasku a daular Boko Haram -Wadanda suka tsira
A yayin da dakarun kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da kuma Najeriya suke samun nasara a yakin da suke yi da ‘yan Boko Haram har suka kwato garuruwa da dama da ‘’yan Boko Haram din suka mayar a karkashin daularsu, kamar su Malam Fatori da Monguno da Gamboru Ngala da Marte da Gwoza da […]
????????????????????????????????????

A yayin da dakarun kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da kuma Najeriya suke samun nasara a yakin da suke yi da ‘yan Boko Haram har suka kwato garuruwa da dama da ‘’yan Boko Haram din suka mayar a karkashin daularsu, kamar su Malam Fatori da Monguno da Gamboru Ngala da Marte da Gwoza da Dikwa da ke jihar Borno, da dai sauransu, Aminiya ta samu damar jin ta bakin wadansu da suka samu damar fitowa bayan an kwato yankunan.
Ita dai rundunar tsaro ta Najeriya ta bayar da sanarwar cewa ta samu nasarar karbe garuruwa 11, tare da yin ruwan bama-bamai a kan dajin Sanbisa da kuma a garin Gwoza, inda ma har ta samu nasarar kashe ‘yan kungiyar sama da 300, tare da kame ababen hawansu da kuma dinbin muggan makamai.
Ba a dade ba ta sake bayar da sanarwar kwato garin Baga da ke yankin karamar Hukumar Kukawa a cikin jihar ta Borno, har ma bayanai suka nuna cewa wadansu maharan sun nutse a cikin Tafkin nan na Chadi. A yayin da su kuma dakarun kasashen Nijar da Chadi ke nasu kokarin wajen kwato garuruwan da ke karkashin ikon Boko Haram a yankunan nasu.
‘Yan gudun hijiran da suka fito daga garuruwan da dakarun ke karon-batta da ‘Yan Boko Haram din sun ce sun tsinci kansu a cikin matsanancin rayuwa a karkashin ikon Boko Haram din saboda tsadar abinci da kayayyakin masarufi.
Malam Babagana, dan asalin garin Dikwa ne wanda dakarun Chadi suka kwato shi kuma a yanzu haka yake gudun hijira a garin Maiduguri, ya fada wa Aminiya cewa, ‘’ Tun lokacin da maharan suka kwace garin Dikwa ina nan a karkashin ikonsu, da yake babu inda zan tafi da ya wuce gidana, duk da cewa ba su kashe ni ba, amma rayuwa ta yi mana tsauri, domin kuwa abinci da sauran kayayyakin masrufi sun yi mana karanci, ga shi duk inda za ka ko ruwa za ka nemo sai ka sanar da su kuma sai sun ga daman barinka. Kai zan iya fada maka cewa sun yi mana daurin talala ne ba ma iya motsawa sai da saninsu. Amma da na samu labarin cewa sojoji sun kwace Gamboru sai ina ta addu’a Allah Ya kawo lokacin da soja za su shigo Dikwa su kwato mana. To Allah da ikonsa sai ga shi sojojin kasar Chadin da suka kwato Gamboru su ne suka karaso suka kwace mana Dikwa kuma har yanzu suna nan.’’
Malam Babagana ya kara da cewa, ‘’Ban fita Dikwa ba sai ranar da na ji sojan Chadi sun shigo da niyyar kwace garin Dikwa, dama ina samun labarin halin da ake ciki a garin Gamboru, saboda haka na san abin dake tafiya, kafin in fito daga Dikwa sojan sun shigo sun kuma dauki dogon lokaci suna musayar wuta a tsakaninsu da ‘Yan bindigan, kafin daga karshe a ci karfinsu su juya baya, aka kashe su, aka kwace makamansu. Amma daga baya ne na samu damar barin garin na Dikwa kuma na gode wa Allah da Ya kubutar da mu daga hannun wadannan azzaluman.’’
Malam Abubakar Ibrahim, wanda shi ma yana daya daga cikin ‘yan gudun hijira daga garin Baga, ya bayyana cewa ya shiga kuncin rayuwa a karkashin daular Shekau, ‘’ A gaskiya na yi farin ciki da soja suka karbi garin Baga, domin tun lokacin da ‘yan bindigan suka kame garimu Wallahi rayuwarmu ta canza saboda rashin abinci da kayayyakin bukatun yau da kullum, ga shi babu abin da mutum zai yi sai sun sani, idan kuma suka san cewa za ka gudu to za su iya kashe mutum. Kafin in bar garin Baga sojojin Najeriya sun shiga kuma sun dauki dogon lokaci suna fafatawa da ‘yan bindigan, amma daga karshe an ci galaba a kansu, har ma sun tsere sun bar wadansu makamansu, suna shiga cikin tafki soja suna bin su. Kai ai a wannan lokacin soja sun yi kokari kuma mun gode musu.’’
Shi ma Malam Algoni Wal-Amire, wanda dan asalin yankin karamar Hukumar Kala-Balge ne, ya ce, ‘’A gaskiya zama a karkashin Boko Haram akwai wahala kuma kana zaune ne cikin zullumi da tsoro domin ba ka sani ba yaushe ne za a ce a kamo ka a kashe ka saboda ka yi wani kuskure kadan, amma a yanzu na samu kubuta, na samu ‘yanci, kuma mun gode wa duk sojojin da suka taimaka aka karbe mana wannan gari namu.’’
Haka shi ma Malam Umaru Baga, yana daya daga cikin ‘yan gudun hijiran da suka kubuto daga karkashin daular Shekau, ya bayyana cewa, ‘’Wallahi mun kasance cikin wani mawuyacin hali a karkashin Boko Haram a garinmu na Baga, domin kuwa ni dan kasuwa ne, ina da shagona a kasuwa, amma in fada maka sun kona wadansu shaguna a kasuwanni da kuma unguwanni, sauran shagunan da ba su kona ba sai suka shiga shagon suka yi kane-kane, wato su suke sayar mana da kayayyakin masarufi, domin ka san babu hanyar da wadansu abubuwa za su shigo ko su fita, dan abin da ya rage ne kawai suke sayar mana da shi. Kuma idan aka ce maka wannan abu ya kare to shi ke nan sai hakuri. Na fada maka rayuwarmu ta tsaya cak, babu wani abin da yake tafiya, babu kasuwanci, babu wata sana’a, haka kawai muke zaune. Sai dai kawai suna tilasta mana mu rika zuwa wajen wa’azinsu, kuma suna cewa suna yin shari’a ta musulunci. To bari in fada maka, babu wani abin da suke yi wanda ya yi kama da hukuncin Ubangiji, idan gaskiya ne su bar mutane su gudanar da harkokinsu mana, ai musulunci ba ya takura wa kowa, amma su sai su takura wa rayuwar mutane kuma su jefa tsoro da fargaba a zukatan mutane, ai wannan ba daidai ba ne.’’
Da ya juya kan yadda sukeb samun abinci da rowan sha kuwa, Malam Umaru cewa ya yi ‘’Boko Haram din suna shiga gida-gida ne suna binciken wanda duk aka samu yana da abinci sai su kasa 3 a bar masa kashi daya, za su fita da kashi biyu, su dauki kashi daya, sai su raba wa sauran mutane kashi dayan. Maganar rowan sha kuwa, wallahi dama can babu ruwa, kuma ga wadannan sun zo su bata garin, domin inda ake samun ruwa jefi-jefi ne, da wuya ka samu Bohol ko rijiyan da yake da ruwa a da, balle kuma a yanzu. Saboda haka muna gudanar da rayuwa ne kawai cikin matsatsi, ai a da garin Baga yana da Jama’a da yawa kuma duk da yawan Jama’a ana wadatuwa da abin da ake da su, amma a wannan lokacin babu mutane, amma kuma babu wani abin da za a ce an wadatu da shi, hatta ma ‘yan Kasuwa zama suke yi a gida, saboda wadannan mutanen sun hana kasuwancin, babu wani abin dake tafiya, to mu mun gode Allah da Ya kawo soja suka kwace mana gari, yanzu kam za mu fara tunanin komawa.’’
Ita kuwa Malama Hauwa Sani, kokawa ta yi da yadda a kowane lokaci ‘yan Boko Haram din ke sanya mata suna yi musu aikace-aikacen gida, ta kara da cewa, ‘’Dafe-dafen abinci da wadansu aikace-aikacen da suke samu muna yi musu yana haifar mini da damuwa da kuma rashin kwanciyar hankali, to mijina baya nan, ba san yadda suka yi da shi ba, ko sun kashe shi ne ban sani ba, ga shi sun kashe mana kasuwanci, babu wani abu da mukeyi sai bauta musu, kuma muna cikin zullumin za su iya kashe mu a kowane lokaci, domin suna daukar mutane daya bayan daya suna zuwa suna harbe su. Akwai wadansu mazan da suka kwashe a Unguwarmu har yanzu babu labarinsu, Wallahi zan gaya maka babu wani harkokin kasuwanci ko cinikayya ko kuma hada-hadan da za a ce mutanen gari ke yi, domin kuwa komai ya tsaya cak, hatta ma abinci ba ko wane ne zai ce maka yana ci sau 3 ko sau 2 a rana ba, a’a mu yanzu kan mun gode da soja suka karbe mana gari, domin kuwa ko ba komai idan muka koma za mu kasance cikin aminci da walwala. Amma ina gaya maka komai ya sukurkuce, kuma a yanzu da kyar muka samu kanmu muka kubuto kafin zuwan soja. Suna cewa suna gudanar da shari’a kamar yadda Allah Ya ce, babu wani abin da suke yi in ban da zalunci da jefa tsoro da fargaba a zukatan mutane.’’