Mun ga tasku a hannun masu garkuwa – Salisu Mu’azu
Salisu Mu’azu Jos, jarumi kuma darakta ne a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. A yanzu shi ne Mataimakin Shugaba na kasa na kungiyar ’yan fim ta Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria wadda aka fi sani da MOPPAN. A kwanakin baya shi ne Shugaban Kwamitin kungiyar MOPPAN da ya sasanta […]
Salisu Mu’azu Jos, jarumi kuma darakta ne a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. A yanzu shi ne Mataimakin Shugaba na kasa na kungiyar ’yan fim ta Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria wadda aka fi sani da MOPPAN. A kwanakin baya shi ne Shugaban Kwamitin kungiyar MOPPAN da ya sasanta jarumi Ali Nuhu da kuma Adam A. Zango bayan sun yi hatsaniya. Idan ba a manta ba a ranar Alhamis din makon jiya ne wadansu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi da kuma wadansu abokan tafiyarsa biyu a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa Jos daga Kaduna. A tattaunawar da Aminiya ta yi da shi, daraktan ya bayyana yadda suka sha garari a hannun ’yan bindigar har na tsawon kwana uku. Ga yadda hirar ta kasance:
Ko za ka bayyana mana yadda wannan al’amari ya faru?
Yadda wannan al’amari ya faru shi ne, mun baro Kaduna zuwa Jos ni da yayana Alhaji Sani Mu’azu da Danlami Yanke-Yanke da kuma Andy Bature, mun je wani taro da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shirya a Kaduna wanda aka gudanar a ranar Alhamis (ta makon jiya) ne, mun zo daidai Jingir a Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato sai ’yan bindiga suka tare mu.
A lokacin muna tafiya sai suka tare hanya, suna dauke da bindigogi suna ta harbe-harbe a sama, hakan ya sa muka tsaya, suka fito da mu sai suka fara dukanmu. Da na ga yayana Sani ya fadi sannan sun ci gaba da dukansa, sai na ce su bari ba shi da lafiya, idan suka ci gaba da dukansa zai iya mutuwa, na ce musu ma daga asibiti muke.
Kafin ka ci gaba, shin sun sa shingaye a kan hanya ne ko kuwa?
Babu wani shinge da suka sa a hanya, sun bazu a hanya ne, suna dauke da tocilan suna haske mu, amma daga baya sun fada mana cewa motarsu tana biye da mu tun daga Saminaka ( Jihar Kaduna), suna kuma sanar da wadanda suka yi garkuwa da mu cewa muna tafe.
Shin iya motarku masu garkuwar suka tare ko sun hada da wadansu motoci?
Iya motarmu kawai suka tare.
Sun kai kamar su nawa masu garkuwar da suka tare ku?
A daidai lokacin da suka tare mu ba zan iya cewa ga adadinsu ba, kasancewar sun riga sun razana mu da harbi a sama, daga baya mun gane cewa sun kai mutum takwas, kuma shekarunsu ba su haura 20 ba, kuma dukkansu Fulani ne.
Bayan sun tare ku a bakin hanya, me kuma ya faru?
Bayan na ce musu yayana Sani ba shi da lafiya ne sai suka ba shi wayarsa, sannan suka tambaye shi ko zai iya tuka mota, sai ya ce musu eh, sai suka ba shi makullin mota ya tafi, mu kuma sun yi tafiya da mu daga wannan lokacin zuwa tafiyar tsawon awa shida a cikin daji, sun tare mu karfe 8:00 na dare, sun kuma sa mun zauna a wani wuri ne da misalin karfe 3:00 na dare.
Daga nan ne suka tambaye mu nawa za mu iya biya, kuma wa za a kira. To, a farko dai na ce musu Naira miliyan daya, na dauka na fada musu kudi mai yawa da zai sa su ji dadi, ai kuwa fadar miliyan daya shi ne dalilinsu na fara dukana ke nan. Tun daga nan na gane cewa ashe hadarin da muke ciki ba karami ba ne.
Bayan sun ajiye ku da misalin karfe 3:00 shin sun ci gaba da tafiya ko a nan kuka yada zango har suka sake ku?
Mun ci gaba da tafiya, muka wuce dajin gaba daya, muka zo wani tsauni da yake karshen dajin, muka hau kan tsaunin muka gangaro kasa, sannan suka kawo mu wajen wani kogo, wanda kamar a nan gidansu yake, idan an fara ruwan sama nan suke shiga, haka idan sun ji wani motsi ma nan suke shiga. Mu dai muna waje, a nan suka ajiye mu tsawon kwana uku a hannunsu. A nan ruwan sama zai kare a kanmu, rana ta fito ta fadi a kanmu, a nan muke yin komai da komai.
Ko kun hadu da wadansu da aka yi garkuwa da su?
A lokacin da muka je mun samu mutum daya, wanda kuma suka harbe shi a gabanmu, ya mutu nan take, sannan suka jefar da gawar, daga baya na gane sun harbe shi ne don ya zama matsayin misali, don su nuna mana irin abin da za su iya yi a kanmu ke nan, idan ba mu ba su hadin kai ba. Sun tambaye shi har sau uku nawa za su iya samu a kansa, amma ya yi musu shiru, shi ne suka harbe shi.
A lokacin da kuke tare da su ko wane irin abinci kuke ci?
Babu batun abinci, kawai idan sun ga alamar mun jigatu, ko muna jin yunwa sai su je su tsinko mangwaro a bishiya su ba mu mu sha, ruwa kuma sai su je su debo ruwan saman da ya kwanta a kasa su ba mu, kuma cikin ikon Allah idan sun ba mu har gode musu muke yi.
Su masu garkuwar wane abinci suke ci ke nan?
Ana kawo musu abinci, ko wani a cikinsu ya fita ya je ya sayo musu abinci, ya kawo musu.
Ko mene ne abin da ya gudana a tsakaninku da wadanda suka yi garkuwa da ku?
Da farko akwai tsoratarwa a tsakaninmu sosai, ganin cewa suna barazanar za su iya kashe mu, sannan muna ganin ko kashe mu suka yi, to gawarmu ma ba za a iya samu ba, sai muka razana.
Amma daga baya da suka ga ana maganar kudi, suka kuma fahimci za a iya samu sai ya zama mun samu sassauci, haka za mu rika zama mu yi hira, kai daya daga cikinmu da yake shi mutum ne mai barkwanci wato Yanke-Yanke da ke Bauchi sai ya zama musu aboki, sai su kira shi ya shiga cikinsu su rika hira suna ta dariya.
Ta bangarenka fa, ko mene ne ya gudana tsakaninka da su?
Maganata da su ba ta da yawa saboda asalina ba mutum ne mai magana ba, to amma tsakanina da su bayan an sasanta a cikinsu sai wani yake ce mini, in roka musu Allah Ya sa su daina, su ma ba a son ransu suke yi ba, a nan ne na sa baki na ce za mu roka musu Allah Ya sa su daina, in har masu dainawa ne. Sai daya ya ce idan kuma ba ma su dainawa ba ne kada mu ce Allah Ya tona musu asiri saboda abin da ba sa so su ji ke nan.
Akwai daya daga cikinsu mai dogon buri da ya ce mini ba zai daina garkuwa da mutane ba sai ya samu Naira tiriliyan 100, sai kuma Allah Ya ba shi sa’a ya yi garkuwa da Buhari da kuma Atiku. A nan ne na kalle shi na ce masa lallai burinka yana da yawa.
Baki ya rabu a kan cewa Naira miliyan 10 kuka bayar kafin aka sake ku, yayin da wadansu suka ce Naira miliyan 3 da dubu 500 ne, ko mece ce gaskiyar magana a kan kudin fansar da kuka biya?
A gaskiya abin da suka fara nema shi ne Naira miliyan 10, na yi ta bugawa da su suka ce ba za su rage ba, domin sun dauka akwai kudin da suna cewa kaza to za a ba su, a haka dai suna kiran waya kuma ana ba su baki, sai suka gane kudin ma kokari ake a samo a hada, sai suka sauko zuwa miliyan biyar, har dai aka tsaya a kan Naira miliyan uku da rabi.
A lokacin da kuke tsare a wurinsu wadanne abubuwa ka rika tunawa?
A gaskiya na tuna abubuwa da yawa, na farko na rika tuna yanzu ko in mutu ko in yi rai ne, haka ya sa na yi ta tuna abubuwan da suka shafi rayuwata da ta iyalina, haka ya sa na rika kallon abin a matsayin fim da muka saba yi. In takaice maka har cewa na yi na samu labarin fim, idan har na samu lokaci zan yi fim a kansa.
A wani hali ka samu iyalinka bayan ka dawo gida?
A nan ne na fi jin tausayin kaina, saboda tun daga can da aka fito da mu na ga ’yan uwa da abokan arziki sai zuciyata ta karye kuma musamman da na shiga cikin gida sai na ga iyayenmu da ’ya’yanmu sun fashe da kuka sai na ji zuciyata ta sake karyewa. Na tausaya musu, na kuma tausaya wa kaina saboda halin da na shiga.
An ga wadansu hotuna a kafafen sada zumunta, an dauke ku kun fito daga cikin wata motar kirar Tifa, yaya aka yi kuka shiga cikin wannan motar?
Bayan sun sake mu sai suka nuna mana hanya, suka ce idan mun bi ta za mu samu wani kauye da za mu iya daukar hayar acaba. Bayan mun bi hanyar ne sai muka fahimci muna ta tafiya ne kawai a daji ba mu san inda muka dosa ba. Muna cikin tafiya ne muka hango mota a cikin daji ana lodin itace, sai muka sanar da su halin da muke ciki bayan mun je wurinsu.
Hakan ne ya sa suka ce mana hanyar da muka bi za ta fito da mu zuwa wani kauye mai suna Mariri ne can hanyar Lere (Kaduna) ke nan. A nan muka gane cewa ashe ma mun kara bata ne. Sai suka ce mu yi hakuri su gama loda itacensu sai su dauko mu su fito da mu inda za mu samu gari. Masu garkuwar sun sake mu ne bayan sun samu tabbacin kudin da muka biya ya shiga hannunsu, a gabanmu suka kasafta kudin.
Yaya batun yin azumi da kuma Sallah fa?
A gaskiya ba mu yi azumi ba, amma za su bar mu mu yi taimama sannan mu yi Sallah.
Mene ne kiranka ga gwamnati da kuma jami’an tsaro kan wannan matsala ta sacewa da kuma garkuwa da mutane?
Abin da na fahimta shi ne a gaskiya kasar nan sai an tashi tsaye da addu’a, domin kariyar Allah ake nema ba ta mutum ba. Na biyu, hukumominmu dole su yi da gaske, su zama suna aikinsu tsakani da Allah. Domin yaran nan Fulani ne amma suna dauke da bindiga kirar AK-47, a ina za su samu? Sun ce mini ma idan mun ce za mu fada wa hukuma, to sun fi mu kusa da hukuma saboda hukuma ba za su ba mu abin da yake hannunsu ba, amma mu ga shi sun ba mu.
Don haka dole a tashi haikan don ganin an magance abin nan, yara ne da ba su fi shekara 20 ba. Akwai matasa da yawa da a yanzu idan suka ji ana samun kudi to za su shiga cikinsu,saboda idan ba a tashi an magance matsalar cikin dan karamin lokaci ba, ina gaya maka kasar nan za ta shiga mummunan hali, musamman ma Arewacin Najeriya.