Mun ga tasku a kwana 50 da muka yi a hannun ’yan bindiga – Mata
A yayin da Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da sasanci tsakaninta da mahara masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa a sassan na jihar, zuwa yanzu, wadansu da ’yan bindigar suka sako sun bayyana kunci da takurar da suka fuskanta a yayin da suke tsare a daji. Wadansu daga cikin wadanda ’yan bindiga masu garkuwa […]
A yayin da Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da sasanci tsakaninta da mahara masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa a sassan na jihar, zuwa yanzu, wadansu da ’yan bindigar suka sako sun bayyana kunci da takurar da suka fuskanta a yayin da suke tsare a daji.
Wadansu daga cikin wadanda ’yan bindiga masu garkuwa da mutanen suka sace a jihar suna cikin murna bayan sako su da aka yi sanadiyar sasancin da aka samu. An ga hawayen murna na fitowa daga idanun ’yan uwan da suka sadu da juna, abin da ba su yi tsammanin faruwarsa ba.
Jihar Katsina kamar sauran makwabtantanta, ta fuskanci hare-haren ’yan bindiga da ke fashi ko sace mutane, wanda hakan ya sa gwamnati ta dauki hanyar sasanci tare da musayar wadanda aka kama a tsakanin bangarorin biyu.
Gwamna Aminu Masari wanda ya bayyana matukar damuwarsa kan hare-hare da aka rika kaiwa a wasu kauyukan jihar, ya ce gwamnati ta fahimci cewa yin sasanci ne kawai matakin da zai kawo sauki tare da samar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Gwamnan da kansa ya jagoranci wadansu daga cikin kusoshin gwamnatinsa domin tattaunawa da maharan a dazukan da suka yi sansani. Daga cikin shugabannin maharan da aka zauna da su akwai Alhaji Masume, Marwana, Leko, Alhaji Ado Maigizo, Alero da Alhaji Lawani.
Daga lokacin da aka yi sasanci zuwa yanzu, maharan sun sako mutum 32 da suka tsare, yayin da gwamnati ta sakar musu mutum 17.
Wadansu daga cikin wadanda aka sako bayan an damka su a hannun Gwamna, sun shaida wa manema labarai cewa rayuwa a maboyar maharan aba ce da ba za su taba mantawa da ita ba.
Safiya Ibrahim daga garin Tone a Jamhuriyyar Nijar na daga cikin wadanda aka kama aka yi garkuwa da su, wadda ta samu kanta daga cikin wadanda aka sako lokacin sasancin.
Ta ce ta kwashe kwana 58 a tsare a hannun maharan inda ta ce lokacin da aka kai hari a kauyensu, an harbi danta mai shekara 22 a kafada. Ta ce tana cikin barci ta ji karar harbe-harben bindigogi. “Farkawata ke da wuya, ina yunkurin tashi sai na ga an nuna mini bindiga. Mutumin ya ce mini in biyo su ko su kashe ni. Sun ingiza keyata muka yi tafiya a kasa har muka je inda suka boye baburansu a can kan iyaka,” inji Safiya.
Safiya ta bayyana halin kuncin rayuwa da suka fuskanta, ita da sauran wadanda aka kamo. “Suna ba ni abinci da safe sau daya, sai kuma gobe. ’Yan kwanakin nan ne ma suka fara ba mu sau biyu a rana. Haka za mu zauna duk tsawon ranar ba abinci ba ruwa,” inji ta.
Matar mai ’ya’ya 8, Safiya ta ce abincin da ake ba su dafaffar shinkafa ce wadda aka sa wa gishiri kawai.
Ita kuwa Zainab Isyaka, wacce ke shayar da jariri lokacin da aka dauko ta daga kauyen Zango na Karamar Hukumar Kankara ta yi kwana 53 da hannun masu garkuwa da mutanen. “Sun kawo hari a garinmu a wata ranar Lahadi da misalin karfe 5 na yamma. Bayan sun gama duk abin da suke yi, sai suka dauke ni tare da wadansu, suka kai mu wani wuri wanda ban iya cewa ga yadda yake a cikin daji. Sun kawo mana buhun shinkafa da gishiri da sauran wasu kayan yin abincin,” inji ta.
Zainab ta ce za ta iya tuna wadansu daga cikin wadanda aka kamo su tare, kamar su Zuwaira, Halima, Zinatu da Hafsat wadanda ta ce yanzu haka suna can cikin dajin.
Sa’ade Garba na daga cikin wadanda aka dauka a garin Shimfida da ke Karamar Hukumar Jibiya, kuma ta yi kwana 16 a tsare. “’Yan bindigar sun tare hanya, hatta da jami’an tsaron sun tare motocinsu. Sun ta yin harbi da bindiga, sai aka ce dukkanmu mu kwanta. Mun kwanta a cikin motar da muke ciki ba tare da muna da wata masaniya ba, ashe wadansu sun sulale sun tsere. Su kansu jami’an tsaron da muke tare da su sun tsere. ’yan bindigar suka zo suka same mu a cikin motar, nan dai suka harbe wata mata. Daga nan sai suka ce ba za su kashe mu ba saboda sun ga dukkanmu mata ne. Sun jera mu a kan layi daya, sai suka kira shugabanninsu ta waya, wadanda su kuma suka ba su umarnin cewa kada su kashe mu amma su kai mu wajensu,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa sun yi ta tafiya a cikin daji, “wata tsohuwa ta ce musu ba za ta iya ci gaba da wannan tafiya a kasa saboda ta gaji, nan take suka harbe ta.” Ta ce lokacin da suka isa maboyar ’yan bindigar, an rarraba su a bangarorin kauyukan da suka fito. Wadanda suka fito daga Shimfida an kebe su waje daya aka ce duk wadda mutanenta ba su kawo Naira miliyan goma na fansa ba, to za a kashe ta ko a mayar da ita baiwa.
Ta ce, sun ci gaba da yin addu’o’i, abin da kadai suke da ikon yi. “Sukan zo lokaci-lokaci su yi ta harbe-harbe cikin iska, suna tsoratar da mu, suna tambayar wadda mijinta ke da kudi. Suna cewa idan ba mu amsa ba, za su ba mu kashi kuma su hana mu yin kuka.”
Ta bayyana rayuwarsu a dajin da cewa tana tattare da kunci da fargaba. Ta ce duk lokacin da ake ruwan sama sai dai su dunkule waje daya su lullube yaransu, su kuwa ruwan ya yi ta bugunsu babu wajen fakewa.
“Mun yi kwana 16 a cikin ruwan sama a wajen. Kullum da safe sai su kawo mana shinkafa da gishiri mu ci. Babu abincin rana balle na dare. Yaranmu ne kadai suke ba wani abu su ci da rana in sun ji suna kuka. Lahadin da ta wuce, sun zo inda muke suka ce duk wadda take kauyen Shimfida ta tashi tsaye, domin za su tafi da mu su kashe. Haka suka gaya wa sauran, daga nan suka nemo baburansu suka dauko mu har zuwa inda aka dauke mu,” inji ta
Wata mai shayarwar mai suna Hassana daga garin Shimfida, ta ce gaskiya rayuwa a irin wannan wuri akwai kunci da firgici, ga yawan karar harbin bindiga, barazanar rayuwa da sauransu. Ta ce akwai hayaniyar koke-koken yara, wadanda ke fuskantar karancin shayarwa daga iyayensu.
“Yaran ba su samun wadataccen nonon da za su sha domin, mu kanmu iyayen muna jin yunwa balle su samu nonon. Ina yi wa Allah godiya da Ya sa ina daga cikin wadanda suka samu sa’ar fitowa daga wannan waje amma akwai saura da yawa da muka baro,” inji Hassana.
Binta wadda ta fito daga Zango, an gan ta tare da yaro dan kimanin shekara uku, wadda ta ce ba danta ba ne amma ita ta rika kula da shi tun lokacin da aka sato su daga kauyen. Ta ce, “Har yanzu ban san halin da iyayensa suke ciki ba, shin suna raye ko sun mutu?”
Wannan shi ne abin damuwar da wannan yarjejeniyar sulhun ke fuskanta, wanda kuma ya kamata a ce an duba domin saukaka radadin da al’ummar da abin ya shafa suke ciki a jihar ta Katsina.