Mun ga wata shi yasa muka yi Idi- ‘Yan Shi’a

Shugaban Mabiya akidar shi’a a jihar Sakkwato Sidi Manniru ya ce sun yi Sallar Idi ne a ranar  Juma’a, 22 ga watan Mayu, domin sun ga watan shawwal bayan sun yi azumin watan Ramadan guda 29. A zantawarsa da Aminiya, shugaban mabiya Shi’an ya ce tsarin da suka bi na ganin wata shi ne wasu […]

Mun ga wata shi yasa muka yi Idi- ‘Yan Shi’a
Shugaban Mabiya akidar shi’a a jihar Sakkwato Sidi Manniru ya ce sun yi Sallar Idi ne a ranar  Juma’a, 22 ga watan Mayu, domin sun ga watan shawwal bayan sun yi azumin watan Ramadan guda 29.
A zantawarsa da Aminiya, shugaban mabiya Shi’an ya ce tsarin da suka bi na ganin wata shi ne wasu mutane ne da suka yarda da su suka sanar da su an ga watan.
Sanarwar ta ce anga watan ne a garin Dukkuma cikin karamar hukumar Isa da garin Yabo da Illela a sanadin haka babu makawa sai su ajiye Azumi su yi Sallah.
Ko kun sanar da Sarkin Musulmi?
Sidi Manniru  ya ce “Yau sama da shekara 20 muke duba watanninmu ba sai watan Ramadan ba, kawai domin jagorarnmu Shaikh Ibrahim Zakzaky ne ya ba da shawarar haka don mu kaucewa rikicin ganin wata.
Wanan rikicin ganin wata  ake da shi a kasa tunda muna da mabiya a ko’ina su duba, su sanar da ‘yan uwansu tun da mu tsintsiya daya muke madaurinmu daya.”
Ya ce ma’anar da aka ba su kan Sallar da suka yi ba haka bane, domin  suna bin ka’idar gwamnati musamman kan cutar coronavirus don har ta’alimi suka dakatar na tsawon wata uku.