Mun ga wulakanci a Kamaru – ’Yan gudun hijira
‘Yan Najeriya da dama da ‘yan Boko Haram suka fatattake su daga garin Gamboru na jihar Borno wadanda suka yi gudun hijira zuwa kasar Kamaru tare da tsammanin za su samu sauki, sun ce a maimakon samun sauki walakanta su aka yi, wanda ya sanya da tsananin ya yi tsanani sai suka samu wata dabara […]

‘Yan Najeriya da dama da ‘yan Boko Haram suka fatattake su daga garin Gamboru na jihar Borno wadanda suka yi gudun hijira zuwa kasar Kamaru tare da tsammanin za su samu sauki, sun ce a maimakon samun sauki walakanta su aka yi, wanda ya sanya da tsananin ya yi tsanani sai suka samu wata dabara da ta tilasta gwamnatin Kamaru ta mayar da su kasarsu. Sun bayyana wa Aminiya cewa,‘Yan sandan Kamaru sun kama ‘yan gudun hijira akalla mutum fiye da hamsin kuma har yau ba a san inda suke ba. Kuma mutane goma sha uku suka rasa rayukansu. Wakiliyarmu ta zanta da shugaban ‘yan gudun hijiran Malam Mustapha Gallambe, wanda yake zaune a sasanin ‘yan gudun hijira na garin Damare. Ga yadda hirar ta kasance;
Aminiya: Yaya aka yi kuka tafi kasar Kamaru?
Gallambe: Sunana Mustapha Gallambe Rijiyar kudi Cirokusko. A ranar Litinin 29 ga watan Augusta na shekarar da ta wuce ne da Boko Haram suka shigo garin Gamboru da ke jihar Borno suka fatattake mu. Daga nan sai muka gudu muka shiga wani gari mai suna Fantakol wanda ke Kamaru, domin gada ne a tsakaninmu da Gamboru. Duk da hakan ma ba mu samu tsira ba, domin a kullum sai ‘yan Boko Haram sun kashe mutane, ga shi kuma ba abin da muke yi. Shi ne wadansu masu keke suka hau suka tafi wani babban garin Kusuri. Mu da ba mu da kudi kuma muka rika takawa har na tsawon kwana uku ni da iyalai na.
Aminiya: Yaya rayuwarku ta kasance a Kamaru?
Gallambe: Ko da muka isa Kamaru babu wani wanda ya karbe mu ko ya tausaya mana saboda halin da muka shiga ciki, face walakancin da muka sha. Gwamnatin Kusuri ta Kamaru ba ta taimaka mana ba ko da da Magi daya ne. Akwai wadansu ‘yan Najeriya da ke shigowa Kamaru ta Yola, wajensu muke zuwa mu karbi lemu sai mu sayar mu samu abin da za mu ci kuma mu biya kudin haya. Ana hakan kuma sai ‘yan Boko Haram suka shiga bin wannan hanyar da muke karbar lemun suna yayyanka direbobi, saboda hakan ne ya sa lemun ya yi wuyar samu.
Sai muka koma Chadi, domin Kusuri din ma boda ne da Chadi. Sai muka koma kasuwancinmu a Chadi, sannan sai mu koma Kusuri mu kwana, haka muka dinga yi. Nan fa idan ‘ya’yanmu sun fita talla idan ba su rage kudi ba sai su ‘yan kasa su rika zaginsu suna cewa su ‘ya’yan Boko Haram ne. Idan kuma dattijo ne sai a ce kai mahaifin Boko Haram ne. Yau da gobe muna fama a hakan. Sai ya kasance da girmanmu sai ‘yan sanda su zo su kama mu su kulle, sannan su caje mu, idan akwai kudi a jikinmu sai su kwace. Idan ba ka da kudi sai ‘yan uwanka za su je su biya Sefa dubu hudu ko biyar, watau a kudin Najeriya Naira dubu bakwai ke nan ,sannan su sake wanda suka kaman.
Matanmu ma na zuwa sayar da albasa, mu ma muna fita nema domin mu hada. Idan suka je kasuwa sai a kama matanmu a ce wai ba a son su saka laffaya. Haka za mu sake komawa mu je mu biya kudi domin a sake su. Idan muka aika yaranmu sayar da ruwan leda (pure water) su ma sai a kama su. Yawan kama ‘yan uwanmu da ‘yan sandan ke yi ya sa muka rasa jarin zuwa debo kaya. Idan mun fita sallar asuba sai mu ga ‘yan sanda sun kewaye mu ba za su yi mana magana ba har sai muna dawowa daga masallaci, sai su ce mu zo, sai su tambayi katinmu na shiga kasa, sai mu ce da su mu ‘yan gudun hijira ne, sannan sai su saka mu a mota a je a kulle mu, bayan kwana biyu ko uku sannan ‘yan uwa su yi belinmu. Idan ko ba ka da ‘yan uwa sai ka yi sama da sati kana nan a kulle.
Akwai wadansu ‘yan sandan da ke zuwa da rana a kan babur, idan sun ga mutum a tsaye sai su ce da shi ya ba da katin shiga kasa, idan babu sai su sa shi a tsakiyar babur din su tafi da shi. Irin wadannan da masu babura ke daukarsu ba mu sake jin labarinsu. Yanzu akalla za su kai mutane hamsin. In dai babur ya dauki mutum shi kenan har gwara wanda ake sawa a mota su muna samun labarinsu.
Haka aka kama yayar matata aka ce in kawo Sefa dubu uku (N600). Sai na dauki dan sanda da muke unguwa daya muka je. Sai aka karbe Sefan kuma aka ce ba za a ba da matar ba.
Kuma idan sun kama mutum daure shi ake yi kafa da hannu a hade, kamar yaron da ke zaune a kan fo. Insha Allah a hakan mutum zai ta zama har gari ya waye a mashigan N’Djemena. Kuma ko an kai wa mutumin abinci ba za a ba da ba. A kullum sai an sa yayar matata ta share filin ofishin ‘yan sandan tas! Akwai yara a tsakanin shekaru sha biyar zuwa ashirin, a kullum sai an yi musu bulala goma-goma haka kawai. Amma mun samu mun karbo ta yanzu.
Mun shiga tsanani sosai da kuma hali na kaka. Sai mu ga an kawo taimako tirela da yawa, muna ji muna gani za a sauke kayan ba tare da an ba mu komai ba, sai ‘yan Kamaru kawai ake ba su. Duk wanda ya ce gwamnatin Kamaru ta taimaka mana mu ‘yan Najeriya karya yake yi.
Da tsananin ya yi yawa, sai na tattara matana da ‘ya’yana muka je wata makarantar gwamnati muka zauna a wurin. Ganin mun koma makaranta da zama sai mutane suka fara zuwa suna tambayarmu dalilin da ya sa muke zaune a filin makaranta. Sai na ce da su ai wannan filin gwamnati ne, ina so in koma kasata Najeriya. Can wadansu ‘yan sanda suka same mu. Muka ce da su ‘yan kasarku sun hana mu mu nemi abinci, muna son gwamnati ta mayar da mu kasarmu Najeriya domin ba mu samun abinci kuma ba mu samun kudin biyan haya kuma idan yaranmu suna rashin lafiya ba mu da kudin saya musu magani. Sai suka ce in bar wurin, na ce ba zan tashi ba, muka yi ta jayayya da su. Sai suka tafi suka sake dawowa. Suka sake cewa da ni in bar wurin, na ce bazan bari ba sai dai idan gwamnatinsu za ta kashe ni ko kuma ta kai ni Najeriya, domin ni ba barawo ba ne.
Sai suka koma suka dawo tare da shugaban ‘yan sandan da kuma shugaban Kusuri da mataimakinsu. Sai suka kira ni suka ce ni ne wanda aka ce in bar wurin nan na ce ba zan bari ba? Na ce eh. Sannan kuma na gaya musu dalilai na. sai suka ce mu nawa ne? Na ce za mu kai dari uku ko dari biyu, sai suka rufe motarsu suka yi tafiyarsu.
Sai wannan dan sandan na fari ya sake dawowa ya ce da ni, me muke rubutawa? Na ce sunanmu kuma a yanzu za mu kai dari shida da sittin da biyar, sai ya ce in ba shi a rubuce, sai na mika masa takardar, ya ce in cigaba da rubutawa. Washegari ya sake dawowa ya ce in ba shi sunayen. A hakan muka samu mutane sama da dubu hudu. Bayan mun yi kwana hudu, sai suka kawo mana tireloli da motocin soja hudu. Da muka shiga, idan mota ta cika a maimakon su bar mu, sai su dauki mutum su wurga a kan tirelar, kamar yadda ake jefa buhun shinkafa. Mutumin da suka wurga zai iya fadawa a kan jariri ko yaro karami. Haka suka dinga yi har sai da muka cika tab a tirelar. A sanadiyar wurga mutanen da suke yi, mutane goma sha uku suka rasa rayukansu. A dayan tirelar kuma mutum daya ne ya rasu.
Sai aka sauke mu a Sauda. Da na fara ganin sojoji har na tsorata, sai da suka ce su ‘yan Najeriya ne sannan hankalina ya kwanta. Na yi kwana biyu a Sauda, daga nan sai aka kai mu Mubi. Sai muka kwana bakwai, amma ana ba mu abinci da wajen kwanciya.
Ran nan sai mataimakin gwamnan jahar Borno marigayi Zanna Mustapha ya yi mana nasiha kuma ya ce da mu mu yi hakuri mota za ta zo ta dauke mu. Washegari sai aka kawo motoci har ana raba mana kudi, sai na ji dadi. Yadda muka isa Yola ke nan. An ajiye mu a sansanin ‘yan bautar kasa na Yola. Aka yi mana tambayoyi. Can aka dauko bargo da katifa da yadi biyar na shadda da bokiti aka ce in yi wanka da kofi da kwano da cokali da sabulun wanka da Omo aka ce nawa ne, haka kuma ‘ya’yana kowa ya samu irin nawa. Sai na ce Alhamdulillahi a can Kamaru ni jaki ne, amma na zo nan na zama rago. Alhamdulillahi!
Wata mata mai suna Lami Abubakar, ita ma ta ba da nata labarin inda ta ce, “ ni ‘yar Kano ce, amma muna zama a Kusuri. ‘Yan Gamboru sun zo gudun hijira a Kusuri, sai manyan Kusurin suka ce ana samun matsala da ‘yan Najeriya saboda yawancinsu ‘yan Boko Haram ne. Sai suka ba da odar cewa duk wani dan Najeriya ya fita ya bar kasarsu. Da yara da manya duk su fita ko kuma za a kamo ka. Idan aka kamo ka za a ci ka tarar Naira ashirin da biyar. Idan kana da katin shiga kasa ka zauna, idan babu kuma sai ka fita. Shugaba Deby ya ce ba ya karbar baki a kasarsa. Paul Biya na Kamaru ya ce yana karbar bako. Amma yanzu Alhamdulillahi mun dawo Najeriya mun ji dadi, domin babu rashin ci kuma babu rashin sha. Hukumar NEMA na kulawa da mu sosai.