Mun gaji da alkawuran yaudara – ’Yan ƙwadago ga Tinubu

Kungiyar ta ce ta gaji da gafara sa, ba ta ga ƙaho ba

Mun gaji da alkawuran yaudara – ’Yan ƙwadago ga Tinubu

Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta TUC, Festus Osifo, ya ce kungiyarsu ta gaji da alkawuran yaudarar da Ma’aikatar Ƙwadago take musu wajen amincewa da bukatunsu.

Daga cikin bukatun, akwai kara wa ma’aikata albashi domin rage radadin cire tallafi da kuma rage wa wasu ma’aikata haraji.

A baya dai Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Simon Lalong, ya ba ma’aikata tabbacin cewa nan ba da jimawa ba gwamnati za ta yi musu karin albashi.

To amma a cikin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Festus ya ce kungiyarsu na son gani a kasa saboda ta gaji da gafara sa.

Ya ce, “A taronmu na karshe da muka yi da Ministan Kwadago, sun fada mana irin wannan, suka ce masa Shugaban Kasa ba ya nan, idan ya dawo zai bayyana ƙarin.

“Amma kuma yau na ga sanarwa na cewa nan ba da jimawa ba, gaskiya mu mun gaji da gafara sa. So muke a fada mana takamaiman lokaci.

“A karshe ’yan Najeriya sun gaji da taruka da alkawura, so muke mu gani a kasa, mun gaji da alkawuran da babu cikawa,” in ji shugaban na TUC.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja