Mun gaji da cewa Najeriya na da damarmaki – Minista
Ministan kula da dabbobi na Najeriya, wanda ya bayyana hakan a taron tattaunawa na shekara-shekara da Daily Trust ta yi na bana, karo na 22 ranar Alhamis.
Ministan kula da dabbobi na Najeriya, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su fara gajiya da faɗin cewa ƙasar nan na da damarmaki, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da ya kamata su fara ganin damar.
Maiha wanda ya bayyana hakan a taron tattaunawa na shekara-shekara da Daily Trust ta yi na bana, karo na 22 ranar Alhamis.
- Babu jihar Arewa da ke da ƙwararrun malamai kaso 50 – Babangida Aliyu
- Hisbah ta kama ’yan mata 16 da ake safarar su a Kano
Ministan ya ce ya kamata manufofin tsare-tsaren harkokin noma su kawo hanyoyin da za a magance matsalolin manoma kan yadda suke noma kawai domin su ci abinci, sai kaɗan suke sayarwa.
Ya ce akwai buƙatar a sauya yadda ake gudanar da harkokin noma da kiwo a ƙasar nan, domin a samu wata hanyar dogarau daban.
Ya kuma koka da yadda matsalar rashin tsaro ta shafi harkokin samar da abinci a ƙasar da sauran ƙalubalen da ke fuskanta.
Minintan ya kuma yi kira da rumgumi harkokin noma a rani da damuna, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai magance ƙarancin abincin, sannan a samu ragin farashinsa.
Duk da haka ya yi kira da a magance matsalar rikice-rikicen manoma da makiyaya, inda ya ce ma’aikatansa na aiki tuƙuru domin magance matsalar a wasu jihohin ƙasar.
Da yake jawabi tun da farko, shugaban Daraktocin Rikunin kamfanin Media Trust, Malam Kabiru Yusuf ya ce alƙaluma suna nuna cewa akwai damuwa a ɓangaren samar da abinci a ƙasar nan.
A jawabinsa a wurin taron mai taken: Samar da abinci: Samar da shi da farashi, ya ce “me ya sa ’yan Najeriya suke shan wahalar samun isasshen abinci da za su ci? Don haka muke nan. Wannan ita ce tambayar.