Mun gamsu da gyaran ilmi a jihar Katsina – Kungiyar SBMC
Kungiyar Masu Ruwa-da- Tsaki a Harkokin Ilimi (SBMC) ta Jihar Katsina ta ce ta gamsu da matakan da Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari ke dauka don maido da martabar ilimi da aka san jihar da shi daga tabarbarewar da yake yi. Shugaban Kungiyar na Kananan Hukumomin Katsina da Batagarawa, Madawakin Majidadin Katsina, Alhaji Sani […]
Kungiyar Masu Ruwa-da- Tsaki a Harkokin Ilimi (SBMC) ta Jihar Katsina ta ce ta gamsu da matakan da Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari ke dauka don maido da martabar ilimi da aka san jihar da shi daga tabarbarewar da yake yi.
Shugaban Kungiyar na Kananan Hukumomin Katsina da Batagarawa, Madawakin Majidadin Katsina, Alhaji Sani Lawal Bakin Kasuwa ne ya bayyana haka, a hirar da ya yi da Aminiya a ofishinsa.
“Gaskiya irin matakan da aka dauka don farfado da ilimin gami da ciyar da shi gaba musamman da aka dauko abin daga tushe da yadda makarantunmu na firamare suke a yanzu, tabbas an samu canji. Misali, ana gina benaye a wasu makarantu, ana gina sababbin ajujuwa,wasu ma makarantar sukutum aka gina. Ka ga ashe za a ce an samu ci gaba matuka, domin da ba a ci gaba da wadannan gine-gine ba, to da yanzu muna nan yaranmu na yawo babu makarantun da za a dauke su; saboda cinkoso. Sannan ga malaman SPower da aka dauka wadanda za su koyar da darussa dabam-daban,” inji shi.
Ya ce babu abin da ya burge su kamar yadda suka ga ’yan makarantar firamare suna muhawara a cikin harshen Ingilishi a lokacin da suka je yi wa Gwamna Masari tashe a cikin watan azumin da ya wuce. “Kuma a gabana aka kawo wa wani yaro takarda nan take ya zana hoton Gwamnan; a inda yake zaune. Wani yaron kuma ya fito duk ya Larabce mu da jawabi. Wato in ka ga irin yadda yaran nan suka yi sai ka ce daga wata babbar makaranta suka fito,” inji shi.
Da ya juya kan zuwan malamai da dalibai a kan lokaci da gwamnatin ta bullo da shi ya ce hakan ya kara taimakawa wajen samun cikakkun darussa, ta yadda babu dama a ce dalibi bai zo makaranta a kan lokaci ba.
Game da kungiyarsu, Shugaban ya ce suna bayar da gudunmawarsu a duk lokacin da aka samu wata matsala ko neman wani agajin gaggawa daga makarantun ba tare da sun jira gwamnati ta kawo nata ba, domin ragewa gwamnatin nauyin da ke bisa kanta. Ya ba da misali da kokarin da suke yi na samar wa rukunin gidaje na Sardauna da ke wajen Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Hassan Usman wata makarantar firamare domin saukaka wa al’ummar da ke wannan yanki daukar yaransu zuwa wasu makarantun da ke nesa.
“Kungiyarmu ta raya Unguwar Sha’iskawa da kewaye, tuni muka yi nisa a kan tallafa wa yaran unguwar musamman ta samar musu da guraben karatu da daukar nauyin wadansu daga cikinsu. Muna yin haka ne domin bayar da tamu gudunmawarga kokarin da gwamnatin Jihar Katsinan ke yi na ciyar da ilimi gaba. Sai dai kuma ka san babu yadda za a yi a ce ba za a rasa samun matsaloli nan da can ba. Misali karin makarantu a wasu garuruwan da kuma ababen zama da sauransu,” inji shi.
Sai ya yi kira ga duk mai ruwa- da-tsaki a harkar ilimi ya fito ya bayar da tasa gudunmawar; ko da kuwa halartar makarantun ne don ganin halin da yara da yanayin koyarwa ke ciki, domin bayar da shawarar irin matakin da ya kamata a dauka.