‘Mun gamsu da kokarin kwato yankunanmu da aka kwace’
Al’ummomin kananan hukumomin Gujba da Gulani da ke gudun hijira a garin Damaturu hedikwatar Jihar Yobe sun nuna jin dadi kan hobbasar da sojoji da hadin gwiwar ’yan banga da ’yan baka ke yi don kwato yankunansu daga hannun ’yan kungiyar Boko Haram. Gwamnatin Tarayya ta dauki alkawari lokacin dage zabe cewa, za a kakkabe […]
Al’ummomin kananan hukumomin Gujba da Gulani da ke gudun hijira a garin Damaturu hedikwatar Jihar Yobe sun nuna jin dadi kan hobbasar da sojoji da hadin gwiwar ’yan banga da ’yan baka ke yi don kwato yankunansu daga hannun ’yan kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin Tarayya ta dauki alkawari lokacin dage zabe cewa, za a kakkabe ’yan bindiga daga yankunan da suka mamaye a jihohin Yobe da Borno da Adamawa don a samu yanayi mai kyau da zai sa a iya zabe a fadin kasar nan, don kowane dan kasa ya samu damar kada kuri’arsa.
Al’ummomin da suka fito daga yankunan da kuma jami’an tsaro sun ce zuwa yanzu aiki ya yi nisa a kokarin da jami’an tsaron ke yi don fatattakar ’yan tada kayar baya daga yankunan da suka mamaye musamman garin Bara hedikwatar karamar Hukumar Gulani da garuruwan Kukuwa Gari da Zango da Gujba a karamar Hukumar Gujba.
Malam Musa Maishayi mazaunin garin Bara ya shaida wa Aminiya a Damaturu cewa, yanzu sun tabbatar cewa Gwamnatin Tarayya da gaske take yanzu don kwato yankunansu daga ’yan tada kayar bayan.
Ya ce dama su sun san ’yan tada kayar baya ba sun fi karfin jami’an tsaro ba ne, an dai sa wata manufa ne ciki, to, amma yanzu da yake ana son cimma nasara ga shi an mayar da hankali a kai.
Shi kuwa Malam Muhammad Lawan Mailemo da ke Buni Yadi cewa ya yi yunkurin korar ’yan bindigar da suka zalunce su suka raba su da muhallinsu da jami’an tsaron ke yi ya yi matukar faranta musu rai domin a da sun zaci ’yan bindigar sun mamaye yankunansu ke nan har illa masha Allahu, ko sai wata sabuwar gwamnati ta zo a ’yanta su.