Mun gamsu da yadda harkar tsaro ta inganta a kwana darin Buhari – Sanata Ndume

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana gamsuwa da nasarorin da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari  ta samu cikin a bangaren tsaro a cikin kwana 100, inda ya ce gwamnatin ta samu gagarumin ci gaba a yaki da Boko Haram da ta addabi Arewa maso Gabas.Sanata Ali Ndume da ke […]

Mun gamsu da yadda harkar tsaro ta inganta a kwana darin Buhari – Sanata Ndume
Mun gamsu da yadda harkar tsaro ta inganta a kwana darin Buhari – Sanata Ndume

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana gamsuwa da nasarorin da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari  ta samu cikin a bangaren tsaro a cikin kwana 100, inda ya ce gwamnatin ta samu gagarumin ci gaba a yaki da Boko Haram da ta addabi Arewa maso Gabas.
Sanata Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya fadi haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, inda ya ce kafin hawan wannan gwamnati yankin Arewa maso Gabas ya shiga mawuyacin halin rashin zaman lafiya, saboda murda-murda da cin hanci da rashawa da sanya siyasa a harkar tsaro da aka yi. Ya ce al’ummar yankin sun shiga mawuyacin hali na rashin tabbas sakamakon yadda suke rasa ’yan uwa da iyaye, a hannun ’yan ta’adda da kuma raba su da matsugunansu.
 Sanata Ndume ya ce kowa ya fahimci cewa babu wani sakaci ko siyasa bayan da Shugaba Buhari ya canja manyan jami’an tsaro inda suka kama aiki gadan-gadan, “A gaskiya wannan canji da aka yi ya fara haifar mana da da mai ido, domin alamu na nuna cewa ana cin karfin ’yan Boko Haram, ko shakka babu an karya lagonsu, don haka wannan kwana 100 ta zo mana cikin nasara,” inji shi.
Ya ce duk da cewa har yanzu ba a samu labarin ’yan matan Chibok ba, amma yana da yakinin cewa za a gan su, saboda yadda jami’an tsaro ke aiki a yanzu, ya roki jama’a su bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai da goyon baya, tare da ci gaba da addu’o’in Allah Ya kawo karshen lamarin.
Game da yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfado da tattalin arziki da suke cikin kudirorin Shugaba Buhari, Sanata Ali Ndume, ya bayyana Shugaba Buhari da “Shugaban da ya san abin da yake yi, domin a yanzu ya shawo kan matsaloli da dama da suka addabi kasar nan, don haka wajibi ne mutanen Najeriya su bai wa Shugaba Buhari cikakken hadin kai da goyon baya ta yadda za a samu nasarar ciyar da kasar nan gaba, mu ma ’yan majalisa muna bai wa Shugaba Buhari gagarumin hadin kai da goyon baya don ciyar da kasar tamu gaba,” inji Sanatan.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista