Mun gamsu da yadda jama’a suka karbi Chibita – Darakta

Daraktan Kasuwanci na Kamfanin CHI Limited, Mista Probal Bhattacharya ya ce kamfanin ya gamsu da yadda jama’a suka karbi lemun Frooty Happy Hour na Chibita. Mista Bhattacharya ya bayyana haka ne lokacin da yake bayani kan shirin jin ra’ayin jama’a da kamfanin ya shirya game da lemun na Frooty Happy Hour a Legas. Ya ce […]

Mun gamsu da yadda jama’a suka karbi Chibita – Darakta
Mun gamsu da yadda jama’a suka karbi Chibita – Darakta

Daraktan Kasuwanci na Kamfanin CHI Limited, Mista Probal Bhattacharya ya ce kamfanin ya gamsu da yadda jama’a suka karbi lemun Frooty Happy Hour na Chibita.

Mista Bhattacharya ya bayyana haka ne lokacin da yake bayani kan shirin jin ra’ayin jama’a da kamfanin ya shirya game da lemun na Frooty Happy Hour a Legas.

Ya ce suna aiki tukuru don tabbatar da sun gamsar da ’yan Najeriya da suke bukatar ababen sha masu kara lafiya da annashuwa. Ya ce, “Kayan sha na Frooty Happy Hour da Chibita ke yi zai ci gaba da gamsar da masu shansa.”

Mutanen da aka tuntuba game da lemun na Frooty Happy Hour sun ce lemun yana samun kasuwa ne sakamakon yadda yake gamsar da su da kuma farashi mai rahusa.

Daniel Elijah wanda dan jarida ne da ke aiki a Legas yana daya daga cikin wadanda aka tuntuba inda ya ce, lemun yana sa annashuwa da dandano mai dadi, kuma yana cikin ababen sha da ya fi sha’awa. “Frooty Happy Hour yana cikin kayan sha da na fi so, yana da matukar dandano mai dadi, kuma yana da rahusan da nake sayen fakiti da dama,” inji shi.

Shi kuwa Joseph Eteng da ke sana’ar zane-zane a Kalaba ya yaba wa lemun Frooty Happy Hour ne kan yadda yake kara lafiya, inda ya ce yana shan lemun don nishadi lokacin da yake aiki ko bayan ya tashi.