‘Mun gamsu da yarjejeniyar zaman lafiya da matasan Sayawa da Hausawa suka kulla’
Tsohon Shugaban riko na karamar Hukumar Tafawa balewa kuma shugaban Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Bauchi (BSADP), Dokta Iliyasu Aliyu Gital ya bayyana jin dadinsa kan yadda matasan Hausawa da na kabilar Sayawa suka hada kansu waje daya domin ciyar da karamar hukumar gaba. Dokta Iliyasu ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa […]
Tsohon Shugaban riko na karamar Hukumar Tafawa balewa kuma shugaban Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Bauchi (BSADP), Dokta Iliyasu Aliyu Gital ya bayyana jin dadinsa kan yadda matasan Hausawa da na kabilar Sayawa suka hada kansu waje daya domin ciyar da karamar hukumar gaba. Dokta Iliyasu ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa a Bauchi, inda ya. ce lokacin da Gwamna Isa Yuguda ya nada shi shugaban riko a karamar hukumar ya samu ana zaman doya da manja tsakanin bangarorin biyu. Amma a cewarsa cikin kasa da shekara biyu sai ga shi matasan Hausawa da Sayawa suna zaman lafiya da juna ba tare da wata tsangwama ba. Dokta Gital wanda ya ce ya ba da himma a lokacin shugabancinsa don sasanta bangarorin biyu ya nuna jin dadi kan yadda ake ci gaba da samun zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu. Kuma ya nuna jin dadinsa kan yadda mutanen karamar hukumar suka fito kwansu da kwarkwata a lokacin aikin bada katin zabe na dindindin da aka gudanar a jihohi 11 na kasar nan a ranakun Juma’a zuwa Lahadin da suka gabata.