Mun gano ƙwayoyi a gidan Sanata — NDLEA

Hukumar NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi a gidan Sanata Oyelola Yisa Ashiru

Mun gano ƙwayoyi a gidan Sanata — NDLEA

Buba Marwa

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi a gidan Sanata Oyelola Yisa Ashiru daga Jihar Kwara, wanda ke zargin hukumar da rashawa.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) ne ya sanar a wani taron manema labarai cewa sun kai samame a gidan Sanatan da ke Ilorin, kuma sun gano ƙwayoyi.

Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Mista Femi Babafemi wanda ya wakilci Marwa, ya bayyana cewa an kama hadiman Sanatan guda uku kuma an gurfanar da su.

Ɗaya daga cikinsu an tura shi gidan yari a watan Yunin 2024.

Babafemi ya yi Allah-wadai da kalaman Sanata Ashiru, na zargin NDLEA da “cin hanci da kuma aikata rashin gaskiya.”

Babafemi, ya ƙara da cewa, Sanatan yana amfani da gidansa wajen hada-hadar miyagun ƙwayoyi.

“An kai samame a gidan Sanatan da ke Ilorin, inda aka gano ƙwayoyi kuma aka kama wasu daga cikin hadimansa guda biyu,” in ji Babafemi.

Ya ƙara da cewar wani daga cikin hadiman Sanatan ya tsere a lokacin da aka kai samamen.

Babafemi, ya ce ɗaya daga cikin manyan yaran Sanatan wanda aka fi sani da ‘Omo Senator’, ya shiga hannu a Offa ɗauke da ƙwayoyi irin su methamphetamine da tabar wiwi.

A cewar Babafemi, Sanatan ya fara jifan hukumar da ƙazafi ne, bayan kayan laifin da aka gano a gidansa.

Ya jaddada cewa NDLEA ta samu taimako daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar na Birtaniya da Amurka bisa nasarorin da ta samu wajen yaƙar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

“Duk da kalaman Sanatan, mun samu tallafi daga ƙungiyoyin duniya. Da wuya a ce hukumar da aka zarga da cin hanci za ta samu irin wannan ƙarbuwa daga ƙasashen duniya,” in ji Babafemi.

NDLEA ta tabbatar wa jama’a cewa ba za ta gushe ba wajen yaƙi da duk wata hanyar fataucin ƙwayoyi, ciki har da shi kansa Sanatan.

Babafemi ya ƙara da cewa, “Ba za mu bar wannan zargi ya hana mu ci gaba da yaƙar miyagun ƙwayoyi ba.”

A gefe guda kuwa, Sanata Kawu Sumaila daga Kano ta Kudu, ya zargi ’yan siyasa da ɗaukar nauyin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa.

Sai dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya dakatar da Sumaila, saboda kalamansa ba su da nasaba da batun da ake tattaunawa a zaman majalisar.