Mun gano adadin shaidar digirin bogi daga Benin da Togo — Ministan Ilimi
Za a kori ma’aikatan da suka gabatar da shaidar karatu ta bogi daga ƙasashen.
Gwamnatin Nijeriya ta ce ta bankaɗo shaidar digiri ta bogi guda 22,739 daga jami’o’i a Jamhuriyar Benin da Togo.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja, yayin wani taron manema labarai.
- Ɗaliban kiwon lafiya da aka sace a Benuwe sun kuɓuta — ’Yan sanda
- Marka-marka a Kuros Riba na kawo cikas ga harkokin kasuwanci
Farfesa Tahir ya ce daga bayanan da ke hannun Hukumar Masu Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), an gano cewa “ɗalibai 21,634 sun gabatar da shaidar digiri ta bogi daga Benin daga 2019 zuwa 2023.
“Mun kuma gano shaidar digiri ta bogi 1,105 daga Togo,” in ji ministan.
Ministan ya ce Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince a kori waɗanda aka gano sun gabatar da shaidar karatu ta bogi daga ƙasashen, waɗanda suke aiki a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.
TRT ya ruwaito Ministan na cewa mutanen sun gabatar da shaidar digiri ne daga jami’o’in da ƙasashen ba su amince da su ba.
Farfesa Tahir Mamman ya ce duk ɗalibin da ya gabatar da shaidar digiri daga jami’o’in da ake koyarwa da Turancin Ingilishi daga shekarar 2017, to sakamakon bogi ya gabatar.
Ministan ya bayyana cewa duk ma’aikatan da aka samu da hannu cikin wannan badaƙala, suna fuskantar matakan ladabtarwa. Sannan sassan da ke kula da aikin, su ma ana yi musu garambawul.
Matakin na gwamnati ya biyo bayan wani bincike da wani ɗan jarida ya yi, inda ya ce ya samu shaidar digiri daga wata jami’a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida, ba kuma tare da ya halarci jami’ar ba.
A watan Disambar 2023 ne, ɗan jaridar na Daily Nigerian, Umar Audu, wanda ya yi basaja a matsayin ɗalibi ya nuna shaidar digiri na bogi da ya samo daga Benin har ma kuma ya shiga sansanin Masu Yi wa Ƙasa Hidima a Nijeriya da wannan sakamakon, bayan ya samu sahhalewar ma’aikatar ilimi.
Lamarinin ya ɗauki hankali sosai a Nijeriya a lokacin, har ma gwamnati ta ce ta ɗauki mataki don magance matsalar, wacce ake gani ta samu karɓuwa ne saboda haɗin bakin wasu jami’an gwamnati.