Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji

Janar Emeka ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro

Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji

Babban Jami’in Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Emeka Onumajuru, ya bayyana cewa saura kiris su gama da jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji.

Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba.

“Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka.

Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro

Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa.

Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a ranar.

An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina

NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini

Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji

Matar aure ta banka wa mijinta wuta