Mun gano masu kitsa zanga-zangar matsin rayuwa — DSS

Burin masu shirya zanga-zangar shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.

Mun gano masu kitsa zanga-zangar matsin rayuwa — DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bayyana cewa ta gano waɗanda suka kitsa zanga-zangar matsin rayuwa da ake shirin gudanarwa a fadin Nijeriya.

Cikin wata sanarwa da DSS ta fitar a Yammacin wannan Alhamis din ta ce ta gano masu daukar nauyi da goyon bayan zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan bana.

Mai magana da yawun DSS, Dokta Peter Afunanya, ya ce suna gargaɗin masu shiryawa ko goyon bayan zangar-zangar da su tabbatar sun sanya kishin ƙasa su janye kudirinsu.

Sanarwar ta ce hukumar ta DSS ta gano cewa wasu ɓata-gari na shirin karkatar da akalar zanga-zanagr da manufar tayar da zaune tsaye a Nijeriya.

Mai magana da yawun na DSS ya kuma yi zargin cewa burin masu kitsa zanga-zangar shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.

“Masu kitsa zanga-zangar na son yin amfani da haddasa hatsaniya domin shafa wa Gwamnatin Tarayya da na jihohi kashin kaji da ɓata musu suna domin haɗa su da talakawa.

“Burinsu shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa duk da cewa ta gano masu kitsa zanga-zangar da masu ba su kuɗaɗe amma hukumar tana bin hanyoyin da doka ta tanada waɗanda ba na amfani da ƙarfi ba domin daƙile zanga-zangar.

Daga ƙarshe hukumar ta nemi iyaye da shugabannin gargajiya da malamai su ja hankalin mabiya da ’ya’yansu da ɗalibai da su guji shiga wannan zanga-zangar.

Sai dai kuma duk da haka hukumar ta ce za ta yi aiki tare da sauran jami’an tsaron ƙasar wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

Aminiya ta ruwaito cewa ita ma Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta yi zargin cewa masu shirin gudanar da zanga-zanga a ƙasar suna so ne su mayar da ita tarzoma kamar yadda ya faru a ƙasar Kenya inda aka kashe mutane da dama tare da ƙone-ƙone.

Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Manjo Janar Buba ya ce duk da cewa ’yan Nijeriya suna da ’yancin yin zanga-zangar lumana, amma sojoji ba za su lamunci duk wani taro da zai rikiɗe zuwa tarzoma ba.

Ya ƙara da cewa rundunar tsaron ƙasar ta bankaɗo shirye-shiryen da wasu marasa kishin ƙasa suke yi na yin amfani da zanga-zangar domin kai hare-hare kan ’yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba da kuma harkokin kasuwanci.

“Yayin da ’yan ƙasa suke da ’yancin gudanar zanga-zangar lumana, ba su da ’yancin tayar da tarzoma,” in ji Janar Buba.

Ya ce, “Wannan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa, za a yi ta ne salon abin da ke faruwa a Kenya kuma ina so na ce, na ɗaya, abin da ke faruwa a Kenya tarzoma ce, sannan na biyu, a yayin da muke wannan magana, ba a warware rikicin ba.

“A nata ɓangaren, Rundunar Tsaron Nijeriya ba za ta naɗe hannu ta ƙyale a gudanar da tarzoma ba a ƙasarmu ba.

“Domin kuwa mun ga yaƙe-yaƙe kuma mun ga yadda tarzoma ta ɓarke a ƙasashen da muka kai wa ɗauki, musamman na rundunar ECOMOG (Economic Community of West African States Monitoring Group) da kuma yadda muka yi aikin wanzar da zaman lafiya a wasu ƙasashe,” a cewar Janar Buba.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe