Mun gano masu shirin wargaza bukukuwan mika mulki —DSS
DSS ta bai wa jama’a tabbacin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, ta bayyana cewa akwai wasu da ke shirin tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan mika mulki da za a yi a wasu jihohin kasar.
A wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis, hukumar ta ce mutanen suna son yi wa aikin jami’an tsaro nakasu ne tare kuma da tayar da hankalin jama’a su jefa tsoro ga ‘yan kasar a lokacin.
- Nada mukamin Karamin Minista ya saba wa tsarin mulki — Keyamo
- Yau ake fara bukukuwan mika mulki ga sabuwar gwamnati
A sanarwar wadda kakakinta, Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta bukaci jama’a da ’yan jarida da ’yan kungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar da su bi ka’idojin da aka tsara a lokacin bikin a ko’ina a fadin kasar.
Haka kuma, sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran karya ko na kanzon-kurege da na zuzuta al’amura da kuma duk wani abu na neman razanarwa.
Hukumar ta kuma shawarci duk wani mutum da ba shi da takardar izini ko ta tantancewa da ya kauce wa shiga wasu wuraren a lokacin da ake bikin.
DSS ta bai wa jama’a tabbacin ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a ko’ina a fadin kasar.
A ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu ne za a yi bikin mika mulki da rantsar da sabon Shugaban Kasa a Abuja da kuma gwamnoni a wasu jihohin Najeriyar.