Mun goyi bayan hukuncin da aka yanke wa Abdul Nyass – ’Yan Tijjaniyya

Shugaban kungiyar Sufayen darikar Tijjaniyya ta Najeriya kuma jagoran Tijjaniya a Jihar Sakkwato Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal ya nuna goyon bayansa da kuma na kungiyarsu kan hukuncin da wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano ta yanke na a rataye Abdul Nyass sai ya mutu kan magangannun batanci da ya yi ga Annabi […]

Mun goyi bayan hukuncin da aka yanke wa Abdul Nyass – ’Yan Tijjaniyya
Mun goyi bayan hukuncin da aka yanke wa Abdul Nyass – ’Yan Tijjaniyya

Shugaban kungiyar Sufayen darikar Tijjaniyya ta Najeriya kuma jagoran Tijjaniya a Jihar Sakkwato Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal ya nuna goyon bayansa da kuma na kungiyarsu kan hukuncin da wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano ta yanke na a rataye Abdul Nyass sai ya mutu kan magangannun batanci da ya yi ga Annabi Muhammad (SAW) a bara.
Farfesa Yagawal ya bayyana cewa, “Majalisar Zartawar kungiyarmu wato Tijjaniya Sufis ta gamsu da wannan hukuncin kuma tana kara ba da goyon baya ga kotun da ta zartar da hukunci ga wannan mutum Abdul Nyass.”
Farfesa Abubakar Yagawal ya yi wannan kalami ne a wata takarda da ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a birnin Sakkwato a ranar Talatar da ta gabata.
Ya kara da cewa “Majalisarmu ba ta amince da duk wani batanci ko suka da wani mutum zai yi wa shugaban halitta Annabi Muhammadu (SAW) ko iyalan gidansa ko shabbansa ba, duk wani mutum da zai soki Annabi, Tijjaniya ba ta tare da shi domin ita martabarsa da girmansa take kokarin karewa. Duk wanda ya saba wa tafiyar Manzon Allah (SAW) mu Tijjanawa ba mu tare da shi.”Ya ce duk mai bin darikar dole ne ya bi hanyar wadanda suka assasa ta waton Sheikh Ahmadu Tijjani da mabiyinsa Sheikh Ibrahim Nyass, wadanda suke matukar son Annabi Muhammadu (SAW) da bin hanyarsa da kare Manzancinsa da damuwa da addininsa, don haka duk mai bin hanyarsu ba zai zagi ko ya soki wadanda suke koyi da shi ba.
Haka ya ce majalisarsu tana bukatar gwamnati a kowane bangare ta samar da wasu jama’a da za su kasance masu tallafawa wajen shiga lungu da sakon kasar nan ta yadda za su tabbatar da zaman lafiya da ganin ana awaitar da addini cikin lumana da gaskiya a guje wa barna a tsakanin mutanen Najeriya.