Mun goyi bayan sulhun Gwamnati da Boko Haram

Assalamu alaikum Editan Aminiya. Muna maraba da sulhu tsakanin Gwamnatin Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram, matukar sun bukaci haka. Idan har hakan zai kawo karshen zubar da jinin al’umma a fadin kasar nan. Domin abin tir da Allah wadai ne ga duk wani dan kasa mai kishinta, irin aika-aikar da wannan kungiyar ta yi […]

Mun goyi bayan sulhun Gwamnati da Boko Haram

Assalamu alaikum Editan Aminiya. Muna maraba da sulhu tsakanin Gwamnatin Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram, matukar sun bukaci haka. Idan har hakan zai kawo karshen zubar da jinin al’umma a fadin kasar nan. Domin abin tir da Allah wadai ne ga duk wani dan kasa mai kishinta, irin aika-aikar da wannan kungiyar ta yi shekara da shekaru. Mu ’yan kasa muna matukar bukatar sulhun matukar zai zama silar samun zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin mutanen Najeriya. Wadansu masu ganin kamar sulhun ba zai haifar da mai ido ba, to wannan makahon tunani ne, domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Allah Ya zaunar da mu lafiya a cikin kasar nan, amin.

Daga Nura Muhd Mai Apple Gusau. 08133376020.