Mun gudanar da taron kasa da kasa ne don gano asalin Hausawa – Farfesa Malumfashi
Malami a Sashin Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce sashin ya shirya taron kara wa juna ilimi na kasa da kasa ne domin a yi nazari da bincike don gano asalin Hausawa da yadda harshen Hausa yake bunkasa. Taron na kasa da kasa da shi ne irinsa na […]
Malami a Sashin Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce sashin ya shirya taron kara wa juna ilimi na kasa da kasa ne domin a yi nazari da bincike don gano asalin Hausawa da yadda harshen Hausa yake bunkasa.
Taron na kasa da kasa da shi ne irinsa na farko da jami’ar ta shirya, yana da taken “Hausawa, Harshe da Tarihi, Da, yanzu da kuma nan gaba.”
Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce “Mun ga lokaci ya yi da za a koma a binciki tarihin Hausawa da harshen Hausa. Wasu sun ce Maguzawa ne, wasu sun ce Yahudawa ne wasu sun ce Fulani ne, wasu sun ce mutanen Afirka ne, wasu sun ce Larabawa ne, wasu sun ce zamanin Annabi Ibrahim suka faro, wasu sun ce zamanin Annabi Nuhu, wasu sun ce zamanin Annabi Musa, wasu ma sun ce mutanen Asiya ne. A takaice dai babu asali guda daya na Hausawa. Wannan shi ne makasudi shirya wannan taro kashi na farko. Kuma muna da burin cimma matsaya dangane da haka.”
Farfesa Malumfashi ya kara da cewa are-aren kalmomi da harshen Hausa ke yi ya samo asali ne daga ci gaba da cudanya da Hausawa suke yi da Larabawa da Turawa da mutanen Asiya da Fulani da sauransu.
Shi ma a nasa jawabin Farfesa Murray Last wanda Baturen Ingila ne da ya koyi Hausa a Najeriya, ya ce “Ya dace a ci gaba da zurfafa bincike dangane da harshen Hausa don na baya su fahimci yadda harshe ke bunkasa.”
Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna, Farfesa Barbanas kuirid ya bude taron. Sannan masana da dama sun albarkaci taron, ta hanyar gabatar da kasidu. Daga cikinsu akwai Farfesa Murray Last da Ibrahim Kwantagora da Ibrahim Malumfashi da Isa Mukhtar da Balarabe Ahmed da Umar Salisu Yakasai da Maikudi karaye da Aliyu Muhammad Bunza da Bukar Usman da Sarkin Sudan Muhammad da kuma masana da dalibai da jama’a da dama.