Mun gurfanar da mutum 41 bisa zargin kashe Malama Ummulkhairi – Uba Sani
Uba Sani ya ce hukumomin tsaro sun samu gagarumin ci-gaba wajen gudanar da bincike kan lamarin.
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta gurfanar da mutane 41 a gaban kotu bisa zargin kisan gillar da aka yi wa Malama Ummulkhairi Usman Aliyu a unguwar Maraban Jos da ke Ƙaramar Hukumar Igabi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayiyar.
An kashe Malama Ummulkhairi tare da ƙona gawarta bayan wasu mutane sun zarge ta da ƙoƙarin sace yara, zargin da daga baya aka tabbatar ba gaskiya ba ne.
Ya ce, “Ya zuwa yanzu, an gurfanar da mutum 41 bisa zargin aikata kisan kai. Sannan an gudanar da bincike kan wasu mutum 41, yayin da aka kuma gurfanar da mutum 30 bisa zargin tara jama’a ba bisa ƙa’ida ba.”
Uba Sani ya ce hukumomin tsaro sun samu gagarumin ci-gaba wajen gudanar da bincike kan lamarin.