‘Mun hada baki da Nafisa ce na yi mata yankan rago’
Wani matashin da ake zargi da yi wa bazawararsa yankan rago a kauyen Daneji da ke Karamar Hukumar Ringim ya mika kansa ga ’yan sanda yana neman a kai shi kotu don a yi masa hukuncin da ya dace saboda ya samu saukin rayuwa. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Jigawa, SP Audu Jinjiri ne ya […]
Wani matashin da ake zargi da yi wa bazawararsa yankan rago a kauyen Daneji da ke Karamar Hukumar Ringim ya mika kansa ga ’yan sanda yana neman a kai shi kotu don a yi masa hukuncin da ya dace saboda ya samu saukin rayuwa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Jigawa, SP Audu Jinjiri ne ya tabbatar da labarin, inda ya ce matashin mai suna Mustapha Idris mai shekara 29 da ake zargi da yi wa bazawararsa Nafisa Hashimu yankan rago, ya dawo gida ne bayan da ’yan uwansa suka kira shi cewa ya dawo gida ana nemansa domin an gano cewa shi ne ya kashe ta.
SP Audu Jinjiri ya ce tuni ’yan sandan farin kaya suka tsare Mustapha inda suke ci gaba da bincike a kansa kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a gaban alkali domin yi masa hukunci.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Mustapha Idris ya ce da yardar bazawararsa Nafisa ya yanka ta domin ita ce ta dauki wukar ta ba shi, ta ce ya yanka ta bayan ta kwanta ta mayar da hannunta baya, shi kuma ya yanka ta saboda ba ya son asirinsu ya tonu.
Ya ce sun dauki matakin haka ne saboda cikin da ya yi mata, kuma ba ya so ta haihu, ita ma ba ta so a ce ta haihu ba aure, inda ya ce sakamakon haka ne ya gudu Legas da zama.
Ya ci ce bayan ya gudu ne sai hankalinsa ya tashi, saboda haka ya dawo gida ya mika wuya domin a hukunta shi, domin a cewarsa ba zai samu kwanciyar hankali ba muddin bai kai kansa wajen hukuma ba.
Mustapha Idris ya kara da cewa ya yi nadamar abin da ya aikata a kan bazawarar tasa saboda haka yana neman afuwar iyayenta.
Ya ce da ma Nafisa a can baya budurwarsa ce, sai bayan da aurenta ya mutu suka sake kulla sabuwar soyayya, inda aka samu akasi ya yi mata ciki. Kuma suka yanke shawarar ya yanka ta saboda asirinsu ya rufu, shi kuma ya yanka ta a bayan gari ya gudu ya bar gawar a gindin wata bishiya.
Da yake bayani, mahaifin bazawarar Malam Hashimu ya ce sun yi mamaki matuka a kan al’amarin, sannan ya ce suna bukatar hukuma ta bi musu kadin lamarin.
Mahaifin matashin, Malam Idris ya ce a iyakacin saninsa bai san dansa da shaye-shaye ba, kuma ya ce da ya samu labarin abin da ya aikata ’yan sanda suna nemansa shi ne da kansa ya kira shi ya dawo gida kuma suka sa shi ya kai kansa ga ’yan sanda.