Mun himmatu wajen ilimantar da mata da kananan yara – Murjanatu Duwan

Aminiya ta samu tattaunawa da Malama Murjanatu Ibrahim Duwan, Shugabar Makarantar nan da ke rukunin gidaje na Goruba Housing Estate a Katsina da ke koyar da Larabci da Ilimin Addini (College of Arabic and Islamic Studies) inda ta tabo wasu muhimman abubuwa da suka shafi koyarwa kamar haka:   Aminiya – In na fahimce ki,dukkan […]

Mun himmatu wajen ilimantar da mata da kananan yara – Murjanatu Duwan

Aminiya ta samu tattaunawa da Malama Murjanatu Ibrahim Duwan, Shugabar Makarantar nan da ke rukunin gidaje na Goruba Housing Estate a Katsina da ke koyar da Larabci da Ilimin Addini (College of Arabic and Islamic Studies) inda ta tabo wasu muhimman abubuwa da suka shafi koyarwa kamar haka:

 

Aminiya – In na fahimce ki,dukkan karatun naki kina yin sa a fannin addini ne?

Malama Murjanatu – Da ma can mun yi karatun addini ne da Larabci a can makarantar ATC (Arabic Teachers College) kuma shi ne muka ci gaba da koyar da yara. A nan ma difuloma ce a kan karatun Larabci da kuma sha’anin ilmin addinin Musulunci. Abin da kawai muka dauka a nan danfodiyo shi ne harshen Turanci. Duk abin da dan boko ke karantawa mun karanta shi amma a cikin harshen Larabci. Mun gama danfodiyo a tsakanin 2000 zuwa 2001. Bayan mun gama shi ma muka dawo babu wajen kara karatu sai dai ci gaba da bayar da karatu. To a wannan dan tsakani ne na samu damar komawa waccan makarantar tawa ta asali a matsayin malama,wato makarantar Abubakar Gumi. Na kai wajen shekara bakwai ina koyarwa a can. 

Sanadiyar samun mata masu kwazo ya sanya har muka yi wani dan zaure a can gidana na bayar da karin karatu,musamman sharhin littattafai wanda karshe abin ya janyo samun wani babban majalisi. A cikin 2005 ne aka bude jami’ar Al-kalam inda na samu shiga a cikin daliban farko, wanda ni ce na nema da kaina don ta farko malamina ne ya nemar mani,wannan kuma ‘yar-uwata ta janyo ni muka tafi,to yanzu ni ce babu kowa wanda ya kawo ni. Saboda haka na yi jami’a tun daga 2005 zuwa 2009. 

Nan ma sai na sake tarar da wani kalubalen fuskantar abokan karatu,domin duk limaman da ke jahar nan wanda nauyi ya hana su zuwa karatu Kano ko Zariya an kuma tattara su acikin ajin. Amma dai aka cigaba da karatun da Allah Ya ba ni nasarar fita da matsayi na biyu, na samu digirina na farko a kan Arabic (B.A Arabic). A shekara ta 2010 sai kuma muka fara samun kalubale a wajen aiki a kan cewa takardar shaidar ilmin ba takarda ba ce saboda da larabci muka yi karatun. Jin haka sai na garzaya makarantar Kimiya da Fasaha ta Hassan Usman a nan cikin garin Katsina,sai na yi difulomar nan da ake kira furofeshinan a kan ilmi na tsawon shekara daya. Bayan na kawo shaidar sai kuma na tarar an daidaita cewa waccan shaidar ma ta ilmin na danfodiyo ya yi amma duk da haka sai ya zamo na kara karfin takardun nawa. Har ila yau, bayan shekara daya da gama wancan sai kuma na ji an ce Jami’ar Umaru Musa sun fara bayar da ilmin digiri na biyu ko kuma in ce Mastas. Sai na ce,na dai gane karatu tamkar daukar kaya don haka bari a sauke shi saboda haka kawai sai na ci gaba a can. A nan kuma na karanta M.A Arabic. 

Aminiya – Kenan duk tsawon wannan lokaci ba a samu matsala da maigida ba? 

Malama Murjanatu:  Gaskiya ban samu wata matsala ba. A nan ma zan yi amfani da wannan dama domin jinjina masa a kan irin wannan gagarumar gudunmuwa da ya ba ni duk kuwa da cewa akwai hidimar gida da ta sauran iyali. 

Aminiya – Wace irin rawa ku mata kuke takawa dangane da bayar da ilmi?

Malama Murjanatu: To Alhamdulillahi. Mata suna da gudunmuwa mai girma wacce za su bayar ga ilmi kuma ilmi ya samu gudunmuwa mai girma. Kuma idan mace tana so ta ci nasarar karatu ko aiki ko kuma duka biyun,to tabbas sai ta fita hakkin gida. Akwai wahala da kuma gwagwarmaya wadanda duka na sha su. Abokiyar zama wacce mafi yawan lokutta muke gani kamar ba a samun wani abin kirki a wajensu to ni sai in ce gaskiya na yi sa’arsu. Abokiyar zama ke korata a cikin dare in ta ji ina wanki saboda ta san gobe ina da makaranta. Kasancewata ta uku  acikin gidan aurena sai na gane cewa girmama wadanda mace ta tarar a cikin gidan.

Aminiya – Yaya za ki auna yadda ake bayar da ilmi a yanzu da su kansu masu bayar da ilmin tare da masu karbar ilmin da shi kanshi ilmin?

Malama Murjanatu:  To! Duka akwai rauni. Misali, ni da na yi karatun ATC ina jin na kai wajen shekara 13 ban gama karatun can ba saboda kullum sai na samu mace 3 ko 4 ta zo mini da karatun ATC, to in da ban yi karatun ba da sai a yi yaya? Saboda haka tsayawa ka yi karatu da kyau shi zai sa ka samu mai kyau, kuma duk lokacin da kake bayarwa kai ma naka na karuwa,shi ya sa ma na yarda da haduwar yin karatu a makaranta. Gaskiya a da an yi karatu, sai dai kawai in kara jan hankalin malamai da cewa a rike amanar koyar da karatu. Matsala ta biyu ita ce ga su masu karbar karatun domin mafi yawa suna tafiya karatu ne domin su zo su yi aiki ,amma in mutun ba manufarsa aiki ba to sai ya tsaya ya yi karatun don ya gane. Ni ganau ce a kan irin wannan kudurin domin da farko niyyar da ta kai ni bai wuce don in zo in koyar a Islamiyya ba,amma ga shi a yau duk wani abin da ake samu a duniya ta fannin karatu na same shi. 

Za mu ci gaba