Mun himmatu wajen ilimantar da mata da kananan yara – Murjanatu Duwan (II)

Daga cikin ayyukan da’awa da muka fara yi ita ta kaimu har yi wa alhazai bita a lokacin zuwa aikin Hajji. Farko ana cewa, ai ba mu zuwa aikin Hajjin sai ga shi tun daga 2003 a lokacin marigayi Umaru na Gwamna aka fara ba ni kujerar Makka, kai sai da ta kai kamar ma […]

Mun himmatu wajen ilimantar da mata da kananan yara – Murjanatu Duwan (II)

Daga cikin ayyukan da’awa da muka fara yi ita ta kaimu har yi wa alhazai bita a lokacin zuwa aikin Hajji. Farko ana cewa, ai ba mu zuwa aikin Hajjin sai ga shi tun daga 2003 a lokacin marigayi Umaru na Gwamna aka fara ba ni kujerar Makka, kai sai da ta kai kamar ma ba za a bar zuwa aikin Hajji ba kuma duk albarkacin karatun. Don haka tunanin cewa a samu karatu don a yi aiki shi ya durkusar da karatu a yanzu. Misalin hakan ya faru a lokacin da ina koyarwa a makarantar ‘yan matan nan yayin da aka kawo wata malama amma ba ta iya hada bakin da za ta koyar ba.

Aminiya:  Wace rawa kike ganin iyaye da al’umma za su iya takawa don ciyar da ilmin gaba?

Malama Murjanatu: Tabbas iyaye suna da rawar da za su taka. Maganar a ce su sa yara makaranta ba ita ce maganar ba a yanzu don an wuce wajen. Illa kawai sai in ce su kula da duka bangarorin ilmin biyu wato na addini da na zamani. Kada a yi tunanin neman ilmin boko kawai ga yara domin wannan ya kawo mana bacin al’umma a Najeriya, saboda mutun bai san addinin shi ba koda kuwa yana son taimakon addinin sai ya zamo bai ma san ta yadda zai taimake shi ba. 

Zuwan aikin Hajji da na rika yi ya sa na ilmantu da wani abu a can kasa mai tsarki domin kafin mu dawo gida ina kai ziyara a wasu makarantu a can inda na ga yadda ake hada koyar da dama da hagu na ilmin,wanda hakan ne ya ba ni damar yin koyi da irin wancan tsarin a nan makarantar inda ake koyar da addini da bokon a lokaci guda. Shi karatun boko bai wuce abin da za a kira sana’a ba, shi kuwa na addini shi zai tserartar da mutun in ma aikin zai yi ya yi na kirki. Kuma yana da kyau mu sani larabci yana da tasiri sosai a wajen karatunmu na addini kamar yadda turanci yake a karatun boko. Sannan kuma ba zan manta ba,dan zaman da na yi bayan gama danfodiyo kafin zuwa jami’a ya sa na yi tunanin bude Islamiyya amma ta koyar da ‘yan mata kawai inda na samu 25 na bude ajin koyon Larabci a cikin 2003 amma saboda tafiya wasu makarantun da yi masu aure ya sa a karshe aka rufe ajin wanda yake da ma dakina ne a gidan miji. 

To a lokacin da ina jami’a wannan tunani na sake bude makaranta ya kara dawo mani. Bayan na nemi iznin maigida sai na je can soshiyal ind a na taba yin shugabancin wata makaranta ta marigayiya Hajiya Lami wacce aka koyar da yaki da jahilci a cikinta,to su suna yin karatu da safe ne ni kuma sai na nemi a ba ni aro in yi da maraice. A karshe ma dai sai na ce bari a yi ta baki daya, sai na je Kano da Kaduna inda na gano wasu makarantu, sannan kuma bisa ga shawarwari har sai na gane cewa,lallai ba a bude makarantar al’umma sai da kafa kwamitin amintattu, saboda haka sai na tunkari dattijo Alhaji Ahmad Bawa Faskari, bayan na gaya masa manufa,sai na samu goyon baya a inda na kawo mutane ya kawo wasu muka hada wadannan ‘yan kwamiti. To bayan ‘yan kwamiti sun zauna sai suka ce to wannan makaranta ba za’ a yi ta falle daya ba kawai ta koyon larabci, sai a yi ta kamar yadda ake yi a ATC kamar yadda ake yin irin su a yankin Funtuwa. Saboda haka,ni ce ta farko wacce ta fara bude makarantar koyon harshen larabci da ilmin addini a nan cikin garin Katsina. 

A takaice, mun yi hadin gwiwa da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya tare kuma da yin rajista a duk inda ya kamata. Makaranta dai ta kankama,ma’ana,makaranta daya amma mai sassa biyu. A nan ne nake mika godiyar mu ga Hajiya Turai ‘Yar’aduwa da Hajiya Halima Nuhu Daura tare da Malam Isyaku Babangida Kankiya wadanda su ne suka hadu har muka samu filin da muka gina wannan makaranta a 2008. Na kuma hada abu biyu a lokaci guda, aikin gwamnati da makaranta. 

Na kuma ajiye aikin gwamnati a 2011, lokacin kuma wannan makaranta har ta fidda dalibanta na farko. Kuma na ajiye aiki ne saboda koyo da koyarwa tare da aikin Da’awah su suka sanya na ajiye aiki ba wai don shekarun sun kai ba. Ganin irin yadda na fara shiga cikin abubuwa daban-dabam har ta kai fagen zan fara yi wa yara kalula tare da aikin gwamnatin ya sa na ga ya kamata in ajiye aikin don in tunkari fuska daya.

Aminiya: A wace mahanga kika ajiye ilmi?

Malama Murjanatu:  To mahangar da na ajiye ilmi shi ne,rayuwa. Ilmi gaskiya shi ne rayuwar mutun, domin duk wanda yake rayuwa babu ilmi to ba shi da bambanci da dabba. Sai dai kafin in yi ban kwana ina da wani sako na musamman da nake so in sar shi ne ga mata. Kada ki ce wai an bar ki baya ,a’a,ba a bar ki ba. Domin akwai makarantu na al’umma har in babu damar zuwa na gwamnati. Wani lokaci ina yawan cewa, mutun ya zo ya tarar da wanda ya wuce shi shi ma ya wuce shi ta fuskar ilmin. 

Har ila yau, mata su rika yarda da kaddara tare kuma da bin ummarni. Da a ce ni da mahaifiyata fada muka yi a kan cewa lallai sai na yi sakandare tun da ita muke so, to na tabbata da ban kai wannan matsayin ba a yanzu. Saboda da yin da’a ga iyaye yana da matukar fa’ida sosai. Kazalika, ina kira ga gwamnati da ta rika kula da irin wadannan makarantu na al’umma domin tamkar kannai ne ga na ita gwamnatin. Saboda haka, ta rika basu duk wani tallafin da ya dace. Nagode.