Mun ji dadin sako alarammomi 123 da aka yi – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya bayyana godiyarsa ga Allah kan yadda aka sako wasu alarammomi ’yan Tijjaniya 123 da sojoji suka kama su a Jihar Yobe watannin baya bisa zarginsu da cewa ’yan Boko Haram ne.Sheikh dahiru ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa […]

Mun ji dadin sako alarammomi 123 da aka yi – Sheikh dahiru Bauchi
Mun ji dadin sako alarammomi 123 da aka yi – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya bayyana godiyarsa ga Allah kan yadda aka sako wasu alarammomi ’yan Tijjaniya 123 da sojoji suka kama su a Jihar Yobe watannin baya bisa zarginsu da cewa ’yan Boko Haram ne.
Sheikh dahiru ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Bauchi a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce alarammomin suna cikin masallaci bayan Sallar asuba ne wasu sojoji suka kewaye su daga bisani suka ce kowa ya shiga mota.
Ya ce “Sun shafe sama da wata biyu a hannun hukumomin tsaro duk hanyoyin da ya kamata mu bi domin ganin an sake su mun bi amma abin ya ci tura,” inji Shehin.
Ya kara da cewa: “Wadannan alarammomi dukkansu ’yan Tijjaniya ne kuma ba su da wani aiki sai zikiri da karatun Alkur’ani kuma a guji taba mutanen Allah domin duk wanda yake wulakanta mutanen Allah to tabbas zai hadu da masifa tun a duniya. Duk manyan mutanen da muka tuntuba wadanda suke rike da mukamai a gwamnati sai kowa ya ce yana tsoron magana domin watakila idan mutum ya yi magana za a iya korarsa daga kan kujerarsa.”
Ya kara da cewa Allah Madaukakin Sarki ba ya son a rika wulakanta mahaddata Alkur’ani hatta matsalar man fetur da muka fuskanta a watannin baya kama wadannan alarammomi ya haddasa ta.
“Don haka muna gargadi ga hukumomi tsaro su fahimci cewa ’yan Tijjaniya sun fi kowa son zaman lafiya a tsakanin al’umma saboda haka babu dalilin da zai sa a rika kama mana mutane haka kawai babu dalili,” inji shi.
Ya ce wasu daga cikin alarammomin sun bayyana masa cewa sun sha bakar walaha a hannun hukumomin tsaron, kuma lokacin da aka sake su wani bawan Allah ne ya saya musu rigunan sawa domin kayayyakin jikinsu sun lalace. Kuma sun yi korafin cewa a wasu lokuta ma ba a ba su abinci.