Mun kafa dokar hana amfani da amsa-kuwwa ga masu tallar magani a Katsina – Shugaba Ono
Shugaban kungiyar masu Sayar da Magungunan Gargajiya da ke amfani da amsa-kuwa (Loudspeaker) ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Musa Abukur wanda aka fi sani da Ono ya ce, sun kafa dokar hana tallace-tallacen maganin ta hanyar amfani da na’urar a wuraren taruwar jama’a da suka hada da masallatai da ofisoshi da makarantu da sauran muhimman […]
Shugaban kungiyar masu Sayar da Magungunan Gargajiya da ke amfani da amsa-kuwa (Loudspeaker) ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Musa Abukur wanda aka fi sani da Ono ya ce, sun kafa dokar hana tallace-tallacen maganin ta hanyar amfani da na’urar a wuraren taruwar jama’a da suka hada da masallatai da ofisoshi da makarantu da sauran muhimman wurare, domin ganin cewa, an daina kuntata wa jama’a tare da ganin cewa an kiyaye dokokin kungiyar.
Kazalika ya ce sun lura cewa, masu tallar sukan yi maganganun batsa da kan ja hankali, musamman kasancewar akwai kananan yara da matan aure da ke cikin gidaje, wadanda sautin ke kai musu. Ya ce a kan haka suka sanya dokar hana bude kararta baki daya. Sannan sun hana yin talla a lokacin Sallah da kuma cikin dare.
Dangane da matsalolin uwar kungiyar ta jiha, Shugaba Ono ya ce shi ne yanzu wanda aka aza wa jagoranci yin sasanci a kan batun jagoranci da ya addabi kungiyar. Ya ce shi dai a bangaren da yake yi wa shugabanci bai yarda suka shiga cikin wannan rikici ba, sai dai kuma a matsayinsa na jagoran kwamitin sasanci zai yi iya kokarinsa don ganin an samu daidaitawa. Alhaji Suleiman ya yi kira ga masu sayar da magungunan gargajiya su ji tsoron Allah a yayin gudanar da kasuwancin nasu yana mai cewa, “Yanzu haka muna nan muna ci gaba da rubuta sunayen duk wani bakon mai maganin da zai shigo cikin jihar, nan.”