Mun kafa kungiyarmu don inganta rayuwar mata da matasa – Magajin Malam
Malam Musa Aliyu Jahun shi ne shugaban kungiyar wayar da kan matasan Unguwar Jahun (Jahun Progresibe Awareness Forum) cikin tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci game da gudunmawar da kungiyar ta bayar a lokacin zaben da aka kammala. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?Magajin Malam: Sunana Malam Musa […]
Malam Musa Aliyu Jahun shi ne shugaban kungiyar wayar da kan matasan Unguwar Jahun (Jahun Progresibe Awareness Forum) cikin tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci game da gudunmawar da kungiyar ta bayar a lokacin zaben da aka kammala. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Magajin Malam: Sunana Malam Musa Aliyu Jahun wanda aka fi sani da Magajin Malam ni ne Shugaban kungiyar Wayar da kan Matasan Unguwar Jahun da ke Jihar Bauchi.
An kafa wannan kungiya ne a shekarar 2010 kuma kadan daga cikin manufofin kungiyar shi ne wayar da kan matasa game da yadda zasu gyara dabi’unsu su zamo mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana kuma su rika bin koyarwar addini sau da kafa. Babu wata al’umma da za ta samu ci gaba a lokacin da matasanta suke ta’ammali da shan miyagun kwayoyi.
Aminiya: Mambobin wannan kungiya sun kai mutum nawa?
Magajin Malam: A gaskiya mambobin wannan kungiya sun kai sama da mutum dubu uku kuma muna da rassa a kananan hukumomin Bauchi da Dass da Katagum da Kirfi da Alkaleri,da sauran kananan hukumomin jiha. Kuma ina tabbatar maka da cewa dukkan mambobin kungiyar kowa yana da sana’arsa wasu daga cikinmu ma’aikatan gwamnatin jiha ne. Kashi 95 cikin 100 na mambobin kungiyar mata da matasa ne domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani, sai tana da matasa masu jini a jika. Matasa su ne sinadarin inganta rayuwar ko wace al’umma a fadin duniya.
Aminiya: Wasu kalubale kuke fuskanta a halin yanzu?
Magajin Malam: Babbar matsalar da muke fuskanta a halin yanzu shi ne mun rubuta takarda wa gwamnatin jiha, amma babu wani sakamako da muka samu har zuwa lokacin da muke wannan tattaunawa. Mun kai ziyara ga shugaban Hukumar Hana Sha da Ta’ammali da Miyagun kwayoyi wato (NDLEA) reshen Jihar Bauchi, sannan kuma mun kai ziyara ga kwamishinan ’yan sanda na Jihar Bauchi domin bayyana masa kadan daga cikin manufofin kungiyarmu. Bayan haka mun ziyarci galadiman Bauchi domin ya sa mana albarka a tafiyar kungiyar a matsayinsu na iyayen kasa. Kuma nan da kwanaki kadan masu zuwa za mu kai ziyara ga Sarkin Bauchi Alhaji Dokta Rilwanu Suleiman Adamu a fadarsa da ke Bauchi.
Matasan Unguwar Jahun da sauran matasan Jihar Bauchi sun amfana da wannnan kungiya domin da yawa daga cikinsu mun koya musu yadda ake sana’o’i kamar kamun kifi. Akwai da yawa daga cikinsu wanda muka sama musu aikin yi.
Aminiya: Mutum nawa suka tuba daga shan miyagun kwayoyi a wannan unguwa ta Jahun?
Magajin Malam: Ina tabbatar maka da cewa akwai dimbin matasa wanda suka tuba daga aitaka miyagun ayyuka sakamakon gudunmwar kungiyarmu don haka kusan kullum bamu da wani aiki sai zama da matasa. Wasu daga cikinsu har sun yi aure sun zamo mutanen kirki a cikin unguwa don haka muke godiya ga Allah bisa wannan nasara da muka samu.
Aminiya: Akwai wani fata da kuke da shi ga sabon gwamnan Jihar Bauchi Barista Muhammed Abubakar dangane ga matasa?
Magajin Malam: Abin da muke so sabon gwamnan Jihar Bauchi ya yi wa dimbin matasan da suka kada masa kuri’a a sassa daban-daban na jihar shi ne batun samarwa matasa hanyoyin dogaro da kai duk gwamnatin da ta sama wa matasa aikin yi to tabbas al’umma za ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma muna fatar alheri ga sabon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da sauran shugabanni al’umma.
Aminiya: Wane sako kake da shi ga matasa?
Magajin Malam: Babban sakona ga matasan Jihar Bauchi da mambobin wannan kungiya shi ne kowa ya kama sana’a domin duk matashin da bashi da sana’a to idan aka ajiye ya ga babu wanda yake kallonsa to tabbas zai dauka. Allah Ya kiyaye.