Mun kafa kungiyarmu don magana da murya daya – Wazobiya

Jigo a kungiyar masu sayar da kayan abinci wacce ake yi wa lakabi da Wazobiya ta kasuwar Abbatuwa da ke unguwar Oko-Oba a Jihar Legas, Mansur Musa Yaro ya ce sun kirkiro kungiyarsu sakamakon rushe kasuwarsu da gwamnati ta yi a kwanakin baya.Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a rumfarsa […]

Mun kafa kungiyarmu don magana da murya daya – Wazobiya
Mun kafa kungiyarmu don magana da murya daya – Wazobiya

Jigo a kungiyar masu sayar da kayan abinci wacce ake yi wa lakabi da Wazobiya ta kasuwar Abbatuwa da ke unguwar Oko-Oba a Jihar Legas, Mansur Musa Yaro ya ce sun kirkiro kungiyarsu sakamakon rushe kasuwarsu da gwamnati ta yi a kwanakin baya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a rumfarsa da ke kasuwar Abbatuwa a Jihar Legas a makon jiya.
Ya ce “Mun kafa kungiyarmu ne saboda rushe kasuwarmu da shugaban karamar hukumar Ijokoro ya yi. Ya zo rana tsaka ya ce ya ba mu ’yan awowi kowa ya kwashe kayansa zai rushe kasuwar. Saboda haka da kowa ya ga uwar-bari da mu da Yarabawa da Igbo da sauran kabilu sai muka hada kanmu muka kafa kungiya don mu yi magana da murya daya.
“Da a rarrabe muke kowa yana da kungiyarsa yana abubuwansa daban-daban. Hakan ya sa ba ma cimma burin da muka sa a gaba ba, amma daga bisani da muka hade wuri daya sai ga shi mun cimma babbar nasara ta kai shugaban karamar hukumar kotu, inda muka samu nasara dangane da lamarin.”
Ya bayyana cewa kungiyar tana da mambobi da yawa wadanda suka hada da masu sayar da shinkafa da wake da tumatirin gwangwani da albasa da yaji da kayan kamshi da sauransu.
Ya ce kungiyarsu ta yi rijista kuma tuni ayyukanta sun yi nisa da suka hada da kwato ’yancin ’yan kasuwa.
“Mun samun nasarori da yawa wadanda suka hada da samun hadin kai da yin magana da murya daya. Ba mu taba samun wata kungiya da aka taba kafawa a kasuwar nan da ke magana da murya daya kamar wadda muka kafa yanzu ba, domin hadin kanmu ya karu ba kamar da ba inda kowa yake tafiya daban-daban. Ka ga wannan babbar nasara ce.” Inji shi.