Mun kafa kungiyarmu ne domin ci gaban kasa
Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa Mutanen Arewa reshen Jihar Edo wato (Arewa Traders Association) ya bayyana manufar kafa kungiyarsu da ciyar da kasa gaba ta fuskar kasuwanci da kuma taimakawa matasa marasa aikin yi. Alhaji Abubakar Ubale ya bayyana hakan ne a wata zantawa da Aminiya a garin Benin, inda ya fara da cewa: “Da farko […]
Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa Mutanen Arewa reshen Jihar Edo wato (Arewa Traders Association) ya bayyana manufar kafa kungiyarsu da ciyar da kasa gaba ta fuskar kasuwanci da kuma taimakawa matasa marasa aikin yi.
Alhaji Abubakar Ubale ya bayyana hakan ne a wata zantawa da Aminiya a garin Benin, inda ya fara da cewa: “Da farko wannan kungiyar mun kafata ne da kyakkyawar manufa na kawo ci gaban kasarmu ba ta nuna bambanci, kungiya ce ta hada kan ‘yan kasuwa da sauran jama’a domin samun ci gaba ta fuskar kasuwanci,” inji shi.
Saboda wannan kuma ya yi kira tare da shawartar ‘yan kasuwa da suke a karkashin wannan kungiyar da kasanci masu rikon amnan wadanda za a yi koyi da su. Ya kara da cewa: “Ya dace mu hada kai a duk, inda muke a cikinin Jihar Edo da kewayenta da kuma kasa baki daya. Domin a yanzu haka muna kokari muga cewa wannan kungiyar ta fadada ta kai ko ina da daukaka martabar ‘yan kasuwan musamman ‘yan Arewa da ke Jihar Edo domin haka ya kamata mu kasance ’yan kasuwa masu gaskiya. don haka ina kira ga gwamnatin jihar Edo akan ta tallafawa yan kasuwanmu na nan jihar da kudade domin samun ci gaba akan kasuwancinsu domin ina ganin, muddin gwamnati tana tallafawa irin wadannan ‘yan kasuwa marasa karfi babu shakka za’a samu ci gaba a kasa,” inji shi.
A karshe Alhaji Ubale ya karkare da sake nanata kira ga ’ya’yan kungiyarsu, inda ya ce: “Ina kara nanata kira da shawartar ’yan kasuwanmu akan su kasance masu da’a tare da girmama juna kuma su fahimci amfanin hada kai da muhimmancin zaman lafiya,’’ inji shi.