‘Mun kafa kungiyarmu ne don taimakawa da karfafa Katsinawa’
kungiyar jinkai da taimakon jama’a ta Katisna dakin kara, ta sha alwashin ci gaba da taimaka wa ilahirin jama’ar Jihar Katsina da suka samu kansu a cikin hali na bukata gwargwadon karfinsu. Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bashir Mustafa ne ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da Aminiya a babban ofishinsu na kasa da […]
kungiyar jinkai da taimakon jama’a ta Katisna dakin kara, ta sha alwashin ci gaba da taimaka wa ilahirin jama’ar Jihar Katsina da suka samu kansu a cikin hali na bukata gwargwadon karfinsu.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bashir Mustafa ne ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da Aminiya a babban ofishinsu na kasa da ke yankin Deidei a Abuja. Ya ce kungiyar, wadda aka kafa a shekarar 2005, sannan ta samu rajista a shekarar 2008, tana tallafa wa jama’a ne daga rassanta da ke jihohi 19 na kasar nan.
Ya ce suna tallafawar ne a bangaren sama wa jama’a aiki a guraben gwamnati; da karfafa su a sana’a da kuma kasuwanci; sai kuma kubutar da su daga hali na fitina da suka samu kansu a ciki.
Daga nasarorin da kungiyar ta samu, inji shugaban, daukar daukan nauyin dalibai da ke cikin hali na bukata a makarantu; da tanadin dakuna 8 a garin Deidei Abuja don tsugunar da al’ummar jihar da ke bakunci a birnin tarayya na dan lokaci, “Sai kuma hana karuwanci ga ’yan mata da muka gano sun fito daga jihar zuwa wasu birane da muke da ofisoshi, don sa su ga hanya tare da maida su ga iyayensu”.
Haka nan ya ce suna sa ido tare da zakulo Katsinawa da suka agaza wajen taimaka wa jama’ar jihar a harkokinsu, inda suke ba su lambar yabo don karfafa musu gwiwa.
A bangaren matsala kuwa ya ce a yanzu haka suna fuskantar matsalar karancin kudin gudanarwa, sai kuma matsalar rashin fahimta da wasu suka yi musu na daukar kungiyar a matsayin ta bangare, ko siyasa, alhali babbar manufarsu ita ce taimakawa da hada kan manyan jihar, ba tare da la’akari da yankin da mutum ya fito, ko jam’iyyar siyasar da yake ciki ba.