Mun kakkabo jirage marasa matuka 42 daga Ukraine —Rasha

Rasha ta yi ikirarin kakkabo jirage marasa matuka guda 42 da suka kai hari a yankin Crimea

Mun kakkabo jirage marasa matuka 42 daga Ukraine —Rasha

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin

Rasha ta yi ikirarin kakkabo jirage marasa matuka guda 42 da suka kai hari a yankin Crimea. 

A safiyar Juma’a Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce 9 daga cikin jiragen an harbo su ne, sauran 33 kuma kashe su aka yi a sararin samaniya ta hanyar lalata manhajar da ke sarrafa su.

Kawo yanzu dai babu bayanin ko harin jirage ya yi barna a Crimea yankin da Rasha da mayar karkashin ikonta daga kasar Georgia a shekarar 2014.

Harin Crimea na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta ke shirin horas da sojojin Ukraine kan tuki da kuma gyaran jiragen yaki samfurin F-16.

Kasar Norway ta yi wa Ukraine alkwarin gudummawar F-16, amma ba ta fayyace adadin ba, ko da yake ana kyautata zaton ba za su kai guda 10 ba.

A watan Oktoba ake sa ran Amurka za ta fara horas da sojojin na Ukraine a sansanint sojin sama na Tucson da ke yankin Arizona.