Mun kama aikin shara mun bar wa masu lafiya bara – Guragun Borno
Gwamnatin Jihar Borno ta dauki guragu 30 cikin su 60 da ta tantance, domin aikin shara a saqo da lungunan da ke garin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar, inda za a riqa biyansu albashin Naira dubu 10 a wata. Shugaban Qungiyar Guragu na jihar. Malam Alfaki Idrisa ya bayyana dalilan da suka sanya suka koma shara […]

Gwamnatin Jihar Borno ta dauki guragu 30 cikin su 60 da ta tantance, domin aikin shara a saqo da lungunan da ke garin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar, inda za a riqa biyansu albashin Naira dubu 10 a wata.
Shugaban Qungiyar Guragu na jihar. Malam Alfaki Idrisa ya bayyana dalilan da suka sanya suka koma shara a maimakon bara. “A gaskiya mun yanke shawarar barin sana’ar bara ce saboda mun ga bai kamata mu dawwama a cikin ta ba, domin a yanzu haka masu lafiya ma sun karbe mana sana’ar barar, su suna yi mu ma kuma muna yi; sai ka rasa wane ne miskini wanda ya kamata a ce an ciyar da shi. Domin duk inda muke tsayawa mu karbi sadaka, to za ka ga masu qafa su ma sun tsaya suna karbe mana dan abin da muke samu. Shi ne sai muka yanke shawarar tunkarar Ma’aikatar Tsaftace Muhali ta jiha muka yi mata wannan kuka,” inji shi.
Ya ce ma’aikatar tsaftace muhalli ta saurare su kuma ta yi masu gwajin mutanensu guda 60, inda aka dauki mutane 30 aiki. “Yanzu haka gwamnati ta bai wa mutanenmu 30 aiki na sharar manyan titunan gari har da lunguna ma kuma ana biyanmu Naira dubu 10 a kowane wata. Yau watanmu biyu 2 ke nan da farawa kuma a yanzu ba mu ba bara, bara ta koma wajen masu qafa, kuma muna sa ran cewa gwamnati za ta sake daukar wasu mutanenmu nan gaba sama da yadda ta dauka a yanzu, domin muna da yawa; mun kai har dubu 3,” a cewarsa.
Shi ma Malam Abdulrahaman Kwankwasiyya gurgu ne wanda ya samu wannan aiki na shara. Ya bayyana farin cikinsa. “Wallahi mun ji dadin samun wannan aikin don ka ga ke nan a yanzu haka gwamnati ta san da mu kuma a duk wata za mu karbi albashinmu bayan mun kammala shara a kowace rana, domin wadansu mutane da matsin tattalin arziki ya same su da kuma wasu ’yan gudun hijira duk sun qwace mana sana’armu ta bara.
To, a halin da ake ciki yanzu mun riga mun yanke shawarar bar musu wannan bara domin mu mun samu aikin shara a yanzu, ba mu ba bara ko roqo, mun kuma gode wa Gwamnatin Jihar Borno da ta ba mu wannan aiki; musanmma Kantoman riqo na ma’aikatar tsaftace muhalli ta jiha, Nasiru Ali Surundi da ya taimaka ya kuma yi ruwa da tsaki wajen daukarmu wannan aiki da kuma raba mu da bara.”