Mun kama litar man fetur na sata 21,000 a Legas – NSCDC

Darajar man ta kai Naira miliyan hudu

Mun kama litar man fetur na sata 21,000 a Legas – NSCDC

Jarakunan man fetur din da NSCDC ta kama a Legas

Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Legas ta ce ta kama lita 21,600 na man fetur daga wadanda ake zargin barayin mai ne a yankin Badagry da ke jihar.

Bayanai sun nuna jami’an sashen yaki da satar mai da ke yankin na Badagry ne suka suka kama man, lokacin da suke tsaka da sintiri wajen misalin karfe 11: na daren Talata.

NSCDC ta ce ta kama jarakuna 720, wadanda kowaccensu ke dauke da lita 30 na man fetur din a cikinta.

Kazalika, Aminiya ta gano cewa an sami nasarar kamen ne a gabar ruwa ta Yafin, lokacin da barayin ke yunkurin yin fasa-kwaurin man zuwa Jamhuriyar Benin.

Wasu majiyoyi sun ce bata-garin, wadanda suka kwana biyu suna cin karensu ba babbaka a yankin sun cika wandonsu da iska lokacin da jami’an tsaron suka yi wa maboyar tasu dirar mikiya ranar Talata.

Jami’in shiyya na hukumar da ke Badagry, CS Akinyemi Ayodeji, ya ce darajar man da aka kama ta kai Naira miliyan hudu.

Ya ce za su mika kayan zuwa hedkwatar hukumar ta jihar Legas da ke unguwar Alausa, domin a fadada bincike.

Kwamandan NSCDC a jihar Legas, Eweka Okoro, ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin Kakakin hukumar a jihar, Olumide Abolurin, ranar Alhamis.

Kwamandan ya ce tuni suka gano mamallakan kayan kuma nan ba da jimawa ba za su fara kamensu.