Mun kama sojan da ya harbe saurayi yayin zanga-zanga a Zariya — Sojoji

Rundunar ta ce fara gudanar da bincike a kan sojan da ya harbe saurayin a Zariya.

Mun kama sojan da ya harbe saurayi yayin zanga-zanga a Zariya — Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama sojan da ya kashe wani matashi yayin zanga-zangar yunwa a Zariya, Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito yadda wani soja ya harbe wani matashi mai suna Isma’il Muhammad a yankin Samaru da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Talata.

Lamarin ya faru ne a titin Sarkin Pawa, inda Muhammad da iyayensa suke zama.

Mahaifiyar mamacin, Zainab Sani, ta ce yana wasa tare da abokansa da ɗan uwansa a ƙofar gidansu.

Ta ce lokacin da suka ga sojojin na zuwa, sai suka gudu tare da rufe ƙofa, amma sojan ya bi su ya harbi kofar ya kashe saurayin.

Babban Kwamandan Runduna ta 1, Manjo-Janar M.L.D. Saraso, ya ziyarci iyalan mamacin domin yi musu ta’aziyya.

Ya tabbatar musu cewar za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan ya nemi duk wanda yake da wata shaida kan lamarin ya miƙa wa hukumomin tsaro.

Saraso ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma ya shawarci al’umma su zauna lafiya tare da kasancewa masu bin doka.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa sojoji na ci gaba da aiwatar da dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Kaduna da Zariya sakamakon tashin hankalin da aka samu a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance a garuruwan biyu.

Ya ce an kai wa sojojin hari ta hanyar jifa da duwatsu tare da ƙona tayoyi duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya.

Nwachukwu, ya ce sojan da ake zargi da kisan matashin, ya harba harsashi ne da nufin tarwatsa masu zanga-zangar, amma tsautsayi ya sa ya kashe matashin.

“Sojan da ya aikata laifin an kama shi kuma ana bincike a kansa,” in ji shi.

Babban Hafsan Soji, Taoreed Lagbaja, ya tura tawaga ta musamman domin ziyartar iyayen matashin tare da yi musu ta’aziyya.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS