Mun kammala duk ayyukan da muka gada – Gwamnatin Katsina

Gwamnatin jihar tana ci gaba da kashe makudan kudi wajen gudanar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al’umma.

Mun kammala duk ayyukan da muka gada – Gwamnatin Katsina

Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina.

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta ce ta samu nasarar karasa dukkanin ayyukan da ta gada daga tsohuwar gwamnatin jihar da ta gabata.

Kwamishinan Ayyuka, Sufuri da Gidaje na jihar, Injiniya Tasi’u Dandagoro ne ya sanar da hakan yayin zanta wa da manema labarai cikin birnin Dikko.

Cikin wani rahoto da gidan Rediyon Freedom ya wallafa, Injiniya Dandagoro ya ce Gwamnatin jihar tana ci gaba da kashe makudan kudi wajen gudanar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al’umma.

A cewarsa, “mun kashe biliyoyin nairori wajen samar da ayyukan ci gaba a jihar tare da kammala dukkan ayyukan da muka gada daga tsohuwar gwamnatin jihar da ta gabata.”