Mun karɓo bashin $1bn don taimaka wa Matatar Dangote — NNPCL
Kamfanin ya ce ana sa ran Matatar Dangote za ta taimaka wajen rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabbatar da karɓo bashin dala biliyan ɗaya, don tallafawa aikin Matatar Dangote lokacin da ta fuskanci matsalar kuɗi.
Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC, Olufemi Soneye ne, ya bayyana hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki kan makamashi a Abuja.
- An kashe ’yan Najeriya 614,937, an sace 2.2m a shekara ɗaya – NBS
- Uba Sani ya mayar wa iyalan Abacha filayen da El-Rufai ya ƙwace musu
“Mun yi dabarar karɓo bashin dala biliyan ɗaya wanda aka tallafawa aikin Matatar Dangote ta shawo kan matsalolin kuɗi da ta fuskanta,” in ji Soneye.
“Wannan tallafi ya bayar da damar buɗe ƙofa ga matatar mai ta farko mallakar ‘yan kasuwa a Najeriya, wanda ke nuna ƙarfin gwiwar NNPC wajen tallafawa haɗin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa don ci gaban ƙasa.”
Ya kuma jaddada cewa ana sa ran Matatar Dangote za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.
A cewarsa, matatar za ta ƙara yawan man da ake tacewa a cikin gida tare da bayar da gudummawa ga tsaron makamashi da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa.
Soneye, ya kuma bayyana wasu nasarori da aka samu ƙarƙashin jagorancin Shugaban NNPC, Mele Kyari, ciki har da sake farfaɗo da Matatar Mai ta Fatakwal da kuma inganta gas ɗin CNG a matsayin makamashi mai tsafta kuma mai rahusa.
“Ƙarƙashin jagorancin Kyari, NNPC ta samu manyan nasarori, ciki har da riba mai tsoka da aka samu karon farko cikin shekaru da dama, wanda ke nuna gagarumin ci gaba a harkar man fetur da iskar gas a Najeriya,” in ji shi.