Mun karya karfin Iran a Afirka – Bin Salman
Ana ci gaba da samun cece-kuce kan jawabin da yarima mai jiran gadon mulkin Saudiyya Muhammad Bin Salman ya yi kan cewa kasarsa ta yi nasarar karya tasirin da Iran da kawayenta ke da shi a Afirka. A wata hira da jaridar Times ta Amurka ta yi da yarima mai jiran gadon na Saudiya, Muhammad […]

Ana ci gaba da samun cece-kuce kan jawabin da yarima mai jiran gadon mulkin Saudiyya Muhammad Bin Salman ya yi kan cewa kasarsa ta yi nasarar karya tasirin da Iran da kawayenta ke da shi a Afirka.
A wata hira da jaridar Times ta Amurka ta yi da yarima mai jiran gadon na Saudiya, Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa ta kai gwauro ta kai mari a Afirka don ganin ta rage tasirin Iran a nahiyar, yadda kawo yanzu ta yi nasarar karya karfin kasar ta Iran a Afirka da kimanin kaso 95 cikin 100.
Kodayake Dakta Zayeed Al-Amri, mamba a cibiyar tsara dabarun mulki da tunkarar matsaloli na kasar Saudiyya ya yi karin haske kan manufar yariman, inda ya ke cewar “abun da yarima ke nufi a nan shi ne tun bayan da ya ayyana shirinsa na tunkarar makiya mai suna Saudiyya ta yi nasarar karya tanadin Iran a Yaman da Somaliya da Djibouti da Sudan kamar yadda ta lalata yunkurinta na kafa makamanciyar kungiyar Hizbollah a Nijeriya da hana Ibrahim Zakzaky yin juyin mulki a kasar”.
To sai dai duk da hakan, wasu na ganin kasar ta Saudiyya na yin azarbabi tare da zuga kanta fiye da kima kan ikirarin da ta ke na karya karfin Iran a Afirka, yadda a daidai lokacin da Bin Salman din ke tsuke bakin aljihu ya ke kuma rage kudaden hannayen jari a Afirka ya ke kuma ayyana yaki kan yada akidar Wahabiyanci, sai dai kasar ta Iran a hannu guda na kara matsa kaimi wajen kulla sabbin huldodi da Afirkan gami da bada guraban karatun ilimin kimiyya da fasaha ga daliban Afirka.
Haka kuma wannan takaddama ta sanya Dakta Amani al-Taweel ta cibiyar bincike Al-Ahram a Masar nuna takaicinta na yadda kasashen biyu ke rura wutar rikicin addini a Afirka don cimma muradunsu na mamaya a yankin. Dakta al-Taweel ta ce “a gaskiya Saudiyya ba abun da ya fi damunta fiye da yada akidar Wahabiyanci a Afirka fiye da kulla huldar kasuwanci da alakar diflomasiyya ta ba ni gishiri in baka manda”.
Manazarta dai na ganin cewa muddin kasashen Afirka ba su raba lamuran addini da na siyasa ko diflomasiyya a alakarsu da kasashen na Saudiyya da Iran ba, to ko shakka babu kokawar yin babakeren da kasashen ke yi da sunan addini kan iya kaiwa Nahiyar ta Afirka ya baro waccan dama, can ta ke fama da rikice-rikicen kabilanci da kalubalen talauci da cutattuka.