Mun kashe Naira miliyan 3 a bikin haihuwar Iyanya – Manaja Ubi
A ranar Alhamis din makon jiya ce matashin mawakin zamani, Iyanya ya cika shekara 27 da haihuwa, inda manajansa Ubi Franklin ya bayyana cewa sun kashe Dala 19,000 (kimanin Naira miliyan uku) wajen dabdalar zagayowar ranar haihuwarsa. A wata tattaunawa da Ubi ya yi da mujallar Encomium Weekly, ya bayyana dalla-dalla yadda dabdalar ta kasance, […]

A ranar Alhamis din makon jiya ce matashin mawakin zamani, Iyanya ya cika shekara 27 da haihuwa, inda manajansa Ubi Franklin ya bayyana cewa sun kashe Dala 19,000 (kimanin Naira miliyan uku) wajen dabdalar zagayowar ranar haihuwarsa.
A wata tattaunawa da Ubi ya yi da mujallar Encomium Weekly, ya bayyana dalla-dalla yadda dabdalar ta kasance, inda ya ce shi ne ma ya shirya dukkan hidimar. Haka kuma ya ce tun farko ya san cewa bikin zai dauki hankalin mutane da yawa, musamman ma yadda manyan mutane suka halarta.
Da aka tambaye shi ko kwana nawa suka dauka suna shirya dabdalar, sai ya amsa da cewa kwana biyu kawai suka yi suna tsare-tsare. Ya kara da cewa shi kansa Iyanya bai san da za a shirya masa wannan kasaitaccen biki ba, bai san irin shirin da aka yi ba, sai da ya je wurin sannan ya tabbatar da idonsa.
Da aka tambaye shi ko zai kiyasta nawa suka kashe a bikin, sai ya amsa da cewa: “Mun kashe Dala 19,000 (kimamanin Naira miliyan uku), a yayin da kuma na ba shi Iyanya kyautar agogon gwal, kirar Roled, wanda kudinsa Dala 25,000 ne (kimanin Naira miliyan hudu).”
Iyanya dai ya fara tashe ne tun bayan da ya buga shahararriyar wakarsa ta ‘Kukere’ shekaru biyu da suka gabata.