Mun kashe wanda yake ƙera wa Hamas rokoki – Isra’ila

Sun ce sun kashe shi ne a wasu hare-hare ta sama da daddare

Mun kashe wanda yake ƙera wa Hamas rokoki – Isra’ila

Sojojin Isra’ila a ranar Laraba sun ce sun kashe daya daga cikin manyan masu kera wa kungiyar Hamas ta Falasdinawa rokokin da take kai mata hari da su.

Isra’ila ta ce ta kashe Muhsin Abu Sina ne a wani hari da dakarunta suka kai ta sama a Zirin Gaza.

Rahotanni sun ce Muhsin yana daya daga cikin kwararrun da ke kan gaba wajen kera wa kungiyar makamai.

Har yanzu dai Isra’ila na ci gaba da ruwan wuta a Zirin na Gaza a matsayin mayar da martani kan hare-haren da Hamas ta kaddamar harin rokoki a Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Sojojin na Isra’ila sun kuma ce sun kashe mayakan Hamas da dama a cikin daren da ya kamata bayan wasu hare-haren da ta kai ta sama.

“Dakarunmu kuma su suka yi amfani da jirage suka kai hari a kan maboyarsu sannan muka kashe ’yan ta’adda da dama,” in ji Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF).

(NAN)

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda