Mun kashe ’yan ta’adda 8,000 a bana — Sojoji
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe ’yan ta’adda 8,034 daga farkon wannan shekara ta 2024 zuwa yanzu.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe ’yan ta’adda 8,034 daga farkon wannan shekara ta 2024 zuwa yanzu.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar a ranar Alhamis.
A cewarsa, an samu nasarar ne a samame daban-daban da sojoji suka kai yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya da kuma sauran yankunan ƙasar.
Ya ce an kama wasu ’yan ta’adda 11,263 da kuma ceto mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su.
“Mun kuma samu nasarar ƙwato makamai 8,216 da harsasai 211,459. Mun kuma daƙile yunkurin satar ɗanyen mai da kuɗinsa ya kai sama da naira biliyan 57,” in ji Buba.
Sai dai duk da irin waɗannan nasarori da rundunar sojin ke ayyanawa, Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro a yankuna daban-daban na ƙasar.
Ko a cikin kwanakin nan an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ’yan bindiga arewa maso yammacin Najeriyar, waɗanda ake kira Lakurawa.
Haka nan ma a baya-bayan nan ƙungiyoyin ’yan bindiga sun riƙa dasa nakiyoyi a kan hanyoyin mota a Jihar Zamfara, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.