Mun kawar da dubban ’yan bindiga daga dazukan Bauchi — Gwamna Bala
Sojoji sun mamaye sansanonin ’yan bindigar, sannan jiragen yaki suka yi musu ruwan bama-bamai da ya hallaka ’yan bindiga da dama tare da lalata sansanoninsu da kayan aikinsu,
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed
Gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya bayyana cewa jami’an tsaro sun wargaza ’yan bindiga sama da 20,000 daga jihar bayan hare-haren sojoji sun wargaza dukkan sansanonin bata-garin a jihar.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai bayan wani taron sirri da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya na yankunan da abin ya shafa, gwamnan ya ce matakin ya biyo bayan wani babban aikin sintiri da ya bankaxo yadda ’yan bindiga suka yi dandazo a fadin dazuzzukan da ke hade Jihar Bauchi da jihohin Filato da Taraba da suke makwabtaka da ita.
Ya kara da cewa aikin sojojin ya kai ga gano manyan matsugunan ’yan bindiga, wanda hakan ya haifar da martani mai karfi daga hukumomin tsaro na kasa da na sama tare da goyon bayan ’yan leken asiri.
Ya bayyana cewa, sojoji sun mamaye sansanonin ’yan bindigar, sannan jiragen yaki suka yi musu ruwan bama-bamai da ya hallaka ’yan bindiga da dama tare da lalata sansanoninsu da kayan aikinsu, lamarin da ya gurgunta ayyukan laifi a cikin dazuzzukan.
- An ci zarafin yara 205 a Gombe a wata 10
- Abba ya zaɓi Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano
- Mata sun rushe shingen tsaro a Filato
“An lalata babura da dama da ’yan ta’adda ke amfani da su, wanda hakan ya gurgunta ikon gudanar da ayyukansu,” duk da cewa, wasu daga cikin bata-garin sun tsere.
Gwamnan ya yaba yadda Shugaba Bola Tinubu da Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa (ONSA) suka saurari koken al’ummar Bauchi kuma suka dauki matakin da ya dace wajen wargaza sansanonin ’yan bindiga sama da 20,000 da ke boye a Dajin Madam da Dajin Jihar Taraba, inda miyagun suka yi gidaje suke zaune tare da iyalansu da kuma janareta dake ba su hasken wutan lantarki.
Ya kuma jinjina wa sojojin da kuma yadda suka kafa sansani a cikin dajin domin qarfafa nasarar da aka samu da kuma hana sake shigowar ’yan fashin da suka gudu cikin dajin.
A cewarsa, gwamnati ta bude kofar mika wuya ga ’yan bindigar da ke ciki da wajen jihar, yana mai shawartar su da su ajiye makamansu su miqa wuya, gwamnati za ta karbe su a tallafa musu, saboda su ma ’yan Nijeriya ne, a matsayin wani bangare na qoqarin karfafa nasarorin tsaro da aka samu kwanan nan.
Bauchi ta ba wa ’yan bindiga dama ta karshe
Gwamnan ya jaddada bukatar samun daidaiton tsarin da zai hada da aiwatar da doka da kuma damar gyara hali.
“Muna kira ga wadanda har yanzu ke boye cikin daji da cikin kogunan dutse da su mika wuya a cikin wannan lokacin. Wannan ba afuwa ba ce, amma dama ce ta komawa da kuma sake shiga cikin al’umma a karkashin kulawar gwamnati,” in ji shi.
Ya ce ana duba shirye-shirye don mayar da wadanda suka mika wuya da iyalansu jihohinsu, kasancewar an gano yawancin wadanda ake zargi ba ’yan asalin Jihar Bauchi ba ne.
Sabbin matakan tsaron al’umma
A matsayin wani bangare na gyare-gyaren tsaro mai fadi, Gwamna Bala Mohammed ya sanar da tsauraran matakan sa ido, ciki har da tattara bayanai na mutane da, sa ido bisa jagorancin jami’an leken asiri, da kuma tabbatar da ayyukan da ake yi a kasuwanni, wuraren shakatawa, da wuraren taruwar jama’a.
Ya ce jihar kuma tana shirin karfafa tsarin tsaro na al’umma ta hanyar daukar ma’aikata da tallafa wa kungiyoyin ’yan banga na gida don kara wa hukumomin tsaro na hukuma. Sabbin matakan, a cewarsa, an yi su ne don hana kirkirar wuraren da ba a kula da su, wadanda za su iya zama mafaka ga masu aikata laifuka.
Ya yi kira ga mazauna yankin da su hada kai da hukumomin tsaro kuma su kasance a fadake, yana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta gudanar da aikin tantance bayanan mazauna yankunan da ke cikin hadari a matsayin wani bangare na matakan karfafa tsaro da hana sake samun maboyar masu laifi a jihar. Ya ce za a gudanar da wannan aikin ne tare da haxin gwiwar Hukumar Kula da Katin Shaida ta Kasa (NIMC) da sauran hukumomin tarayya da suka kamata domin tabbatar da samun ingantattun bayanai da kuma sa ido kan duk wani motsin jama’a a yankunan da ke da hatsari.
A cewarsa, wannan shiri na da nufin kawar da wuraren da ba a kula da su, wadanda masu laifi sukr iya amfani da su wajen kafa sansanoninsu da kuma kai hare-hare kan al’ummomin da ke kewaye. Wannan mataki, a cewarsa ya biyo bayan nasarar ayyukan tsaro da aka yi wadanda suka wargaza sansanonin ’yan bindiga da dama a yankunan dazuzzuka a cikin Bauchi da jihohin makwabta, wanda hakan ya haifar da kwanciyar hankali a wuraren da abin ya shafa.
Ya yaba da kokarin hukumomin tsaro, da kuma yadda ci gaba da ayyukan suka kawo cikas ga harkokin kungiyoyin masu laifi.
Ya kuma sake nanata kiransa ga ’yan fashin da suka gudu da su mika wuya a lokacin da ya bayyana a matsayin dama ta wucin gadi don zaman lafiya, yana mai jaddada cewa ba afuwa ba ce amma dama ce ta barin tashin hankali da kuma sake hadewa cikin lumana.
Gwamna Bala ya kara tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana kara himma wajen hadin gwiwa da sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro da hukumomin tarayya don ci gaba da gudanar da ayyuka da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a fadin Jihar Bauchi.