Mun kawo tsarin da za a kiwata rago da abincin N3,000 a shekara — Sarkin Muri
Ya ce sabuwar fasahar zata taimaka wajen rage rikicin makiyaya da manoma.
Mai martaba Sarkin Muri, Alhaji Abbas Tafida wanda ya yi fice wajen kokarin kawo maslaha ga matsalar tsaro musamman kan rikicin makiyaya da manoma, ya ce neman sani da amfani da ci gaban zamani zai habaka harkar kiwo sannan ya kawo maslaha. A tattaunawarsa da Aminiya, Mai Sarkin ya ce sun kawo wani tsari da za a kiwata rago da abincin Naira 300 a shekara:
Yallabai ganin kai manomi ne kuma makiyayi, a al’ada idan aka ce manomi da makiyayi sai a rika tunanin fada da gaba a tsakaninsu, yaya aka yi ka hada biyun?
- Kotu ta ba da belin ‘Dansarauniya’ a kan N1m
- Lafiyar mutumin da ya shekara 67 bai yi wanka ba ta ba likitoci mamaki
To ai ni Sarki ne kuma shugaban al’umma, ka ga dole in zama da bambanci da marasa hankali. Duk wanda yake kiwo ba ya noma bai yi tunani mai kyau ba, haka shi ma wanda noma ba ya kiwo. Don haka maganar rikici a tsakaninsu hauka ce kawai ba wani abu ba.
A matsayinka na shugaban al’umma, me kake ji shi ya kawo matsala a tsakaninsu?
Zan fara amsa wannan tambayar da ba ka wani labari. Wani dan uwana ne ya zo ya samu yayanmu da matansa suna fada duk sun ce ya rubuta musu takardar saki.
Sai ya samu takarda ya rubuta cewa na samu Adama da Yashanu mahaukata biyu suna fada, don haka wancan ta ce a sake wancan, wancan ma ta ce a sake wancan, kuma na san alkali ba ya hukunci ga mahaukata. Sai ya ba su suka rike kuma dukkansu ba su yi karatu ba.
Don haka a takaice ba a cewa mara hankali yana da hujja. Da farko idan an ce manomi, ana nufin wanda yake shuka ya girbe ya ci abincinsa, kuma daga cikin abin da yake ci akwai nono da zai hada da fura.
Mai kiwon kuma shi ne mai kiwon shanu ya samu nama da nono, shi kuma dole yana bukatar gero a furarsa da dawa da zai yi tuwo. Ka ga abin da ya hada su ya fi abin da ya raba su yawa. Ka ga ke nan aikina a matsayina na shugaba shi ne in wayar da kan mutane su zama sun san abin da suke yi, su san hujjar abin da suke yi.
Dole a matsayinmu na shugabanni mu mayar da mutane masu hankali. Don haka ina ganin kawai wannan laifi ne na shugabanni.
Ka bude gona ta zamani, a matsayinka kana noma a zamance, an sha fama da rikice-rikice kan rashin burtali, shin kana ganin zaunar da shanu a waje daya kamar yadda kake yi zai bayar da abin da ake bukata?
Zai ma fi bayar da abin da ake bukata sama da yawon kiwo. Maganar burtali wato hanyoyin da shanu suke bi ke nan. Ita ruga ai kullum ruga ce, amma yadi na canjawa da zamani. Don haka babu yadda za a yi tafiyar jiya a ce ita ce za ta dawo a yau.
Akwai bukatar shanu su samu hanyar da za su bi a tsakanin wurare na kusa da kusa, wannan kuma maganar hankali ce. Amma yanzu ka shuka ciyawa ka girbe ka ba shanu ya fi riba, ya fi alheri ya fi mutunci. Don haka maganar mai shanu ya zauna a wuri daya kuma ya zama asara wannan jahilci ne, shanun da suke yawo sun fi zama asara domin yau za su koshi gobe su ji yunwa, sai a karshe ka ga ba su karu ba.
Amma yanzu akwai ciyawar da za ka shuka ta zamani wadda za ka shuka hekta daya ta rike maka shanu 30. A yadda nake lissafi a gonata, kowace saniya tana cin Naira 40 a rana. Rago kuma yana cin Naira 10 a rana. Idan ka lissafa ka sayi dan rago ka turke shi daga Layya zuwa Layya kwana 300 ke nan, idan yana cin Naira 10 a rana, ka kashe Naira 3000 ke nan a shekara.
Kai kuma za ka iya sayarwa a Naira 30,000. Don haka wannan lissafin ya fi. Lissafi kuma ai mutum ne. Allah Ya ce a Kur’ani, Yana bayar da hikimarSa ga wanda Ya so, kuma duk wanda Ya ba hikima, Ya ba shi alheri mai yawa. Don haka duk sana’ar da mutum yake yi dole ne ya nemi hikimarta ya nemi fasalin da zai fi riba mai kyau.
Wadanne abubuwa kake nomawa a gonarka da kake ganin ya kamata saura su koyi da kai?
Duk abin da nake yi ina so a zo a koya a yi amfani da su. Aikin hankalin ne, aikin hikima ce da habaka riba. Wadanda nake kusa da su kuma duk sun gane. Yanzu mun kawo injina wadanda za su yanka ciyawa su danne ta a sa a buhu.
Kowane buhu zai dauki kilo 50 kamar yadda ake sa siminti, kuma bai fi buhun siminta girma ba, ciyarwar ce aka danne. Yadda aka danne ta za ta shekara biyu ba ta lalace ba. Kuma za a dauke ciyawar a mota babu wahala domin tirela daya za ta dauki tan 30 kamar yadda take daukar siminti.
Kuma buhun ciyawar nan zai kai Naira 700, kuma zai ciyar da shanu hudu a rana. Ma’ana ko za a dauki ciyawar a kai maka har da ribarmu, za ka ciyar da shanu a Naira 150 a rana. Ka je ka tambaya me amfani da dusa a kiwo ka ji.
Yau buhun dusa Naira 7000, kuma buhu ba zai wuce shanu 10 ba a rana. Ka ga ke nan yana kashe 700 a saniya daya a rana. Mu kuma za mu ba ka ciyawa, sannan za mu nuna maka yadda za ka yi da kanka, kuma za mu sayar maka da inji.
Niyyarmu ita ce muna yin kasuwancin Annbawa, wato mu yi kasuwancinmu da alheri domin mu samu riba a Lahira.
To amma bayan saukin da za a samu, yaya batun nono da nama da za a samu?
Idan aka samar da abinci mai kyau, ai dole nono ya habaka. A yanzu wannan ciyawar idan saniya ta ci, za ta samar da lita wato babbar kwalba ta madara biyar zuwa 10 a rana. A yanzu babu Fulanin da suke wuce lita biyu a rana.
Don haka madarar da ake samu za ta karu, saniya za ta kara kyau. A yanzu dai kawai kamar yadda ake cewa ne amarya ba ta laifi, to wannan tsarin kamar amarya ce, kowa kawai ya zo ya bi wannan amaryar shi ne alheri a gare shi.
Wane kira kake da shi ga shugabanni da kuma manoma da makiyaya?
Shugabanni su ji ni. Farilla ce ga shugaba ka nemi sani, ka tabbatar sanin nan kuma alheri ne ga mutanenka, sannan ka tabbatar ka kai sanin nan ga mutanenka. Dole kowane shugaba ya zama fitila a cikin mutane mai haskaka musu.
Don haka duk ’yan uwana sarakuna, su sani rawanin namu ne, amma hankali shi ne rawani ba zanin da aka daura ba. Don haka mu fito mu nemi sani, mu tabbatar kuma mun kai sanin ga mutanenmu.
Su kuma manoma da makiyaya ina kira gare su kada kowa ya bata lokacinsa, babu wani batun wai wannan manomi ne wannan makiyayi. Kowa ya yi duka biyun. Kashin shanunka ka yi shuka a wajen, gonarka kuma shanunka su kwanta.
Inda kuma akwai fitina, mun kawo tsarin da za ka kawo abinci sannan ka dauki kashin shanun ka kai gona. Don haka ba dalilin bata lokaci. Alheri ya zo, sani ya zo, sani kuma daga Allah yake zuwa. Duk inda sani ya zo kuma ka ki dauka, shi ma gefen kafirci ne domin addini hikima ne.
Sai dai ana tsoron akwai yanayin girman fili da ake bukata wajen zaunar da shanu a waje daya, wanda ake tunanin zai yi wahala?
Shi ma wannan an yi fasali mai kyau. Da wannan ciyawar, fili kadan da a da bai fi ya rike shanu biyu ba, yanzu zai rike shanu 30. Sannan ka yi lissafin filin daga nan za ka yi lissafin shanun da za ka rike.Wanda ya rike shanu biyar suka ba shi dan saniya kowace shekara, suka ba shi nono bokiti a kowace saniya, ya fi wanda yake cikin daji da zai rike shanu 100 ya samu bokiti daya.
Yaya kake ganin wannan tsarin naka zai magance matsalar rashin tsaro?
Akwai rashin sana’a. Shi ya sa aka ce a yi hikima, hikimar farko in mun ba yaranmu karatu da sani, kowa zai yi hukuncin sanin abin da yake daidai da alheri a gare shi. Don haka tun farko ma jahilci ne ke sa mutum ya shiga inda ba alheri ba ne a wajensa.
Sannan ba za mu cire hannun gwamnati ba, dole gwamnati ta fito ta duba ta yarda da gaskiya, gaskiyar kuma ita ce a da ana cewa soja suna tawaye suna kwace mulki, yanzu fa rashin kula ya kai idan ba a yi a hankali ba, talaka ne zai yi wa soja tawaye.