Mun kona jabun magunguna ne don inganta kasuwanci a kasar nan – Kwastam

A ranar Talatar da ta gabata ce jami’an Hukumar Kwastam na shiyyar Kaduna da Katsina da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC), suka kona kayayyaki na milyoyin Naira da suka kama a mabambantan lokuta daga hannun masu yunkurin shigowa da su ba bisa ka’ida ba.  Da yake zagayawa da […]

Mun kona jabun magunguna ne don inganta kasuwanci a kasar nan – Kwastam

A ranar Talatar da ta gabata ce jami’an Hukumar Kwastam na shiyyar Kaduna da Katsina da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC), suka kona kayayyaki na milyoyin Naira da suka kama a mabambantan lokuta daga hannun masu yunkurin shigowa da su ba bisa ka’ida ba. 

Da yake zagayawa da manema labarai domin gani da ido a hedkwatar Hukumar Kwastan da ke Katsina, Kwanturolan Hukumar na Katsina, Olusimire Akinde Kayode ya ce wasu daga cikin kayayyakin da suka kama sun hada da shinkafa da man alga da maganin sauro da kayan gwanjo. 

Sauran kayan da hukumar ta kama kuma ta kone da suka kai katan dubu 7 da 250, su ne  maganguna daban-daban wadanda wa’adinsu ya kare aiki, inda ya ce da sun fada hannun jama’a ba a san irin barnar da za su yi ba. Haka kuma daga cikin kayayyakin akwai masu hadari kamar na sanya maye da suka hada da really edtra da Kodin na ruwa da taramol da maganin karfin maza. Ya ce, an yi asarar kudin shiga har na Naira milyan 580 da dubu 737 da 400.

Kamar yadda ya ce, ba doka ba ce a rika shigowa cikin kasa ta kan iyaka bayan kuma ba su dauke da alamar amincewa sannan wa’adin aikinsu ya kare, amma ake samun marasa tunani da kishi suna shigowa da su cikin kasa. Ya ce hakan yana kara jefa matasa cikin miyagun ayyuka.

Kwantorolan ya yi kira a fito a yaki irin wadannan mutane masu kokarin kassara kasar nan. “Duk maganin da za a sha a tabbatar likita ne ya rubuta shi,” inji shi Sai ya kara nanata cewa hukumar ba mai durkusar da harkokin kasuwanci ba ce kamar yadda wadansu ke tunani, musamman a kan iyakokin kasar nan, abin da kawai take nema shi ne, duk wanda zai shigo da kayan kasuwancinsa to ya bi ka’ida. Daga nan sai ya yaba wa Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman bisa goyon bayan da yake ba jami’ansa kan yaki da wadannan miyagun ayyuka.

Da yake magana a madadin Babban Daraktan Hukumar NAFDAC, jami’i mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Ibrahim Sabo Adamu ya yaba wa Hukumar Kwastan a Jihar Katsina a kan irin yadda take sanya ido a kowane gefe don ganin cewa, hatta hukumar da yake yi wa jagoranci tana taimaka mata.

A jawabin, Mai martaba Sarkin Katsina, wanda ya samu wakilcin Sarkin Fadan Katsina, Alhaji Abdulkadir Sama’ila, ya yaba da irin hadin kan da ya gani a tsakanin jami’an tsaron da ke jihar. Sannan ya tabbatar musu cewa, kofar masarautarsa a bude take a kowane lokaci domin sauraren kowace irin gudunmawa da suke nema.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno