Mun kudiri aniyar kakkabe fyade a Jihar Kano – Matar Kwamishina

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?Hajiya Saliha: An haife ni a karamar Hukumar batgarawa a Jihar Katsina. Na yi karatun firamare a can. Sannan na shiga Sakandiren Gwamnatin Tarayya ta Bakori. Bayan na kammala sai na sami gurbin karatu a Jami’ar Bayero Kano inda na karanta fannin tattalin arziki na kammala a 1995. Na yi aure […]

Mun kudiri aniyar kakkabe fyade a Jihar Kano – Matar Kwamishina
Mun kudiri aniyar kakkabe fyade a Jihar Kano – Matar Kwamishina

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?
Hajiya Saliha: An haife ni a karamar Hukumar batgarawa a Jihar Katsina. Na yi karatun firamare a can. Sannan na shiga Sakandiren Gwamnatin Tarayya ta Bakori. Bayan na kammala sai na sami gurbin karatu a Jami’ar Bayero Kano inda na karanta fannin tattalin arziki na kammala a 1995. Na yi aure a 1996 inda a yanzu nake da ’ya’ya takwas.

Aminiya: Wadanne ayyuka kungiyarku ta matan ’yan sanda ke yi a Jihar Kano?
Hajiya Saliha: Kamar yadda aka sani muna da kungiya ta matan ’yan sanda da muke kira POWA, muna ayyuka da yawa da suka shafi ci gaban matan ’yan sanda. Muna da tsare-tsare da suka hada da taimaka wa ’ya’yan kungiyar ta hanyar koya musu sana’o’i da taimaka musu da dan abin da za su yi sana’ar.  Akan ba matan ’yan sanda dama su gina shaguna, inda kowace mai shago za ta bayar da misalin Naira dubu daya ga kungiya. Daga haka muke samun dan abin da ake gudanar da kungiyar da sauransu.

Aminiya: A kwanan nan an ji kungiyarku ta yunkuro don yaki da masu fyade, me ya ja hankalinku ga yin haka?
Hajiya Saliha: Lokacin da maigidana ya kama aiki a Kano bai yi wata biyu ba sai ga rahotannin yin fyade sama da 70 a gabansa. Hakan ba karamin tayar min da hankali ya yi ba. Ganin cewa akwai dama da nake da ita a matsayina na shugabar kungiyar sai na ga akwai bukatarmu mu bayar da tamu gudumawar. A nan sai muka gano cewa masu yi wa yara fyaden wasu ’yan uwa ne wasu ma’aikatan gida ne da makwabta da sauransu. Bincikenmu ya gano cewa mafi yawan yaran da ake yi wa fyaden ’yan talla ne. Hakan ya sa muka shirya gangamin wayar da kai zuwa kauyuka. A yanzu mun fara da karamar Hukumar Madobi ganin cewa yawancin yara masu talla da ke shigowa Kano daga can suke. Da muka je mun tara iyayen yara mun nuna musu hadarin da ke cikin talla, domin daga nan ake lalata yaran. Muka nuna musu yadda talla ke tasiri wajen illata rayuwar yaran, kasancewar a kullum suna haduwa da maza barkatai suna mu’amala da su. Irin hakan ma yakan jawo yara da sun yi aure, sai auren ya mutu saboda sun tashi ba su tsoron maza ballantana su girmama mazajensu.  Kasancewar harkar tabbatar da fyade yana da wahala idan ba wanda ya yi fyaden ne ya yi ikirari ba, don haka a wannan gangamin wayar da kan da muke yi muna sanar da iyaye kan mahimmancin daukar matakin gaggawa idan har abin ya faru (wanda ba ma fata) ma’ana akwai bukatar a yi gaggawar zuwa asibiti don yin gwaji.
Sai batun shaye-shaye, inda aka bayyana cewa Kano ta fi sauran jihohin kasar nan yawan masu tu’ammali da miyagun kwayoyi. Kowa ya san matsayin Kano a Najeriya, ita ce kamar cibiyar Arewa. Hakan yana damunmu kwarai da gaske.

Aminiya: Zuwa yanzu wadanne nasarori kuka samu kan wannan lamari na fyade?
Hajiya Saliha: Alhamdulillahi, za mu iya cewa muna da kararrakin fyade masu yawa da muke bi a kotuna, kuma akwai alamun nasara a ciki. Ganin cewa mu iyalan ’yan sanda ne hakan ya jawo mutane suna sakin jiki da mu suna fitowa su gaya mana matsalolinsu. Kin san wasu suna tsoron su tunkari ’yan sanda da irin wadannan batutuwa, domin a tunaninsu ba za a yi musu yadda suke so ba. Akwai mutumin da ya zo ya same mu yake gaya mana cewa wata hudu da suka wuce an yi wa ’yarsa fyade, amma tsoro ya hana shi sanar da hukuma. Kafin mu fara wannan lamari akan dauki lokaci wajen yin shari’ar fyade a kotuna, amma yanzu ’yan sanda (tunda mazajenmu ne) suna kokarin shigar da kara tare da tsayawa wajen ganin an gurfanar da wanda ake zargi gaban alkali. Haka likitoci a nasu bangaren suna ba mu hadin kai kwarai da gaske, da zarar an kai musu matsalar ba sa bata lokaci wajen ba da sakamakon bincikensu.

Aminiya: Wace shawara kike da ita ga iyaye ganin cewa su ne tubali na farko na tarbiyyar ’ya’yansu?
Hajiya Saliha: Iyaye kullum su ake fara zargi da zarar ’ya’ya sun lalace, idan kuwa haka ne ya kamata a matsayinmu na iyaye mu kula tare da sanya ido a kan tarbiyyar ’ya’yanmu. Iyaye mata su kula da yadda muke aiken ’ya’yanmu, bai kamata mu rika aikensu barkatai ba. Dole mu kula da wurin da za mu rika aikensu da lokutan da suka dace, saboda akwai batagari da suke labe suke son su yi amfani da irin wannan dama su far wa ’ya’yanmu. Mu kula da yadda muke sakar wa direbobi ’ya’yanmu da sunan kai su makaranta. Haka mu kula da makwabtanmu da ba su da iyali. Mu kula da mu’amalar ’ya’yanmu da malamansu, domin a yanzu haka akwai shari’ar da muke da ita, inda wani malami ya bata dalibansa mata uku. Haka mu kula da nisan gidajenmu da makarantun ’ya’yanmu, domin akwai inda za ki ga a kan hanyar zuwa makaranata aka yi wa yara fyade. A kula da yanayin hanyar makarantar yaran, shin akwai ’yan iska a hanyar kuma akwai bukatar a matsayinmu na iyaye mu rika zama da ’ya’yanmu muna sanar da su abin da rayuwa take ciki, wannan kuwa ya hada har da iyaye maza. A matsayinka na uba ya kamata a ce kana samun koda awa daya a rana da za ka zauna da ’ya’yanka, hakan zai sa ka san halin da suke ciki da fahimtar rayuwarsu. Idan da shakuwa tsakaninka da ’ya’yanka za ka yi saurin gano alamun canjin rayuwa a tare da su. Batun shaye-shaye ma idan aka samu iyaye masu kula, akan yi saurin gano hakan tun farko-farko kafin al’amura su kai ga lalacewa. Haka akwai bukatar maza su rika sanya ido a kan lamuran gidajensu. Bincike ya nuna cewa mata suna dillancin kwayoyi suna kaiwa gidajen matan aure. Ya kamata mutum ya kula da canje-canjen halayen matarsa musamman yawan barci da sauransu.  Game da yadda ake boye batun fyade mun san cewa ba kowa ne zai iya fitowa fili ya ce an yi wa ’yarsa fyade ba, saboda a wasu lokutan ’yan uwa na kusa da iyayen yaran da ake batawa ne ke yi. Yaya za a yi mace ta fito ta ce kanenta ko kanen mijinta ya yi wa ’yarta fyade ko ta ce mijinta ya lalata mata ’ya (agola). Amma duk da haka muna so iyaye su rika fitowa suna fadi don ta haka ne kadai za a dakile aukuwar yawan fyade a cikin al’ummarmu.