Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tinubu ya ce nan ba da jimawa ba rikicin manoma da makiyaya zai zama tarihi a Najeriya.

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da yawa.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake rattaba hannu kan takardar yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa nama a duniya mai suna JBS S.A.

Tinubu, ya ce sabon ƙudirinsa na janyo masu zuba jari a harkar kiwon dabbobi daga ciki da wajen ƙasar nan zai magance yawaitar rikicin manoma da makiyaya.

Har ila yau, ya ce ƙudirin zai kawar da fatara da yunwa daga Najeriya da kuma bunƙasa ci gaban tattalin arziƙi.

Tinubu, ya buƙaci kamfanin ya yi nazarin ɗimbin albarkatun da za su bayar da damar zuba jarin dala bilyan 2.5 a harkar kiwo a Najeriya.

Ya ce sanya hannun jarin zai ciyar da ɗimbin al’ummar Najeriya gaba, duba da ƙwarewar da kamfanin yake da shi a faɗin duniya wajen tabbatar da wadatar abinci.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe