Mun kusa sanar da sunayen wadanda suka sace kudaden Najeriya- Gwamnatin Tarayya

Ministan Shara’ar Najeriya, Abubakar Malami (SAN) ya ce “Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci bangarorin gwamnati su tattara sunayen wadanda suka yi wandaka da kudin gwamnati, domin a tabbatar da hukuncin da kotun Legas ta yanke, inda ta bukaci a sanar da sunayen wadanda suka wawushe kudin kasar.” Hakanan kuma, kotun ta bukaci gwamnatin ta bayyana […]

Mun kusa sanar da sunayen wadanda suka sace kudaden Najeriya- Gwamnatin Tarayya

Ministan Shara’ar Najeriya, Abubakar Malami (SAN) ya ce “Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci bangarorin gwamnati su tattara sunayen wadanda suka yi wandaka da kudin gwamnati, domin a tabbatar da hukuncin da kotun Legas ta yanke, inda ta bukaci a sanar da sunayen wadanda suka wawushe kudin kasar.”

Hakanan kuma, kotun ta bukaci gwamnatin ta bayyana wa ‘yan kasa yadda aka kwato kudaden, da kuma yawan kudin da aka kwato wajen kowa.

Malami ne ya sanar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da tawagar wata kungiyar mai rajin kare hakkin dam Adam (SERAP) a ofishinsa na Abuja, sannan kuma babban daraktan kungiyar, Adetukunbo Mumuni ya fitar da bayanin.

A cewar Mumuni, “Mun tattauna sosai da Malami. Daga cikin abin da muka tattauna, akwai batun cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi biyayya ga hukuncin da kotun Legas ta yanke.

Mumuni ya kara da cewa, “Malami ya shaida mana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Minsitan shara’a, Ministan Kudi, Hukumar EFCC, da sauran hukomomi da ke aiki wajen kwato kudaden da aka sace da mu tattara sunayen wadanda aka kwato kudi a wajensu, domin mu yi biyayya ga hukuncin kotun, wanda mai shara’a Hadiza Rabiu Shagari ta yanke a Legas,” inji shi.