Mun kusa yin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano — Abba

Gwamnan ya ce ba zai yi katsa-landan a zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar a jihar ba.

Mun kusa yin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano — Abba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi nan bada jimawa ba.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan yayin wani taro da shugabannin jam’iyyar NNPP a gidan gwamnati da ke Kano.

Gwamnan, ya ce za a gudanar da zaɓen ne bisa hukuncin Kotun Koli da ya bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.

Ya jaddada muhimmancin mutunta doka da kuma riƙon gaskiya da adalci a gwamnati.

Gwamna Yusuf, ya yi alƙawarin cewa za a yi zaɓen cikin gaskiya da adalci, tare da gayyatar jam’iyyun adawa su shiga, saboda gwamnatinsa ba za ta yi katsa-landan a zaɓen ba.

“Mun bari tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi sun kammala wa’adinsu, duk da matsin lamba, saboda girmama doka,” in ji shi.

Ya bayyana cewa shirye-shiryen zaben na ci gaba kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), ta bayyana.

Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa zaɓen zai gudana nan bada jimawa ba, sannan jam’iyyar za ta zaɓi ‘yan takara na shugabanni, mataimakan shugabanni, da kansiloli a faɗin kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya nuna ƙwarin gwiwa cewa mafi yawan mutanen Kano za su goyi bayan jam’iyyar NNPP a zaɓen da za a gudanar.