Mun kwace babbar tashar nukiliyar Ukraine —Rasha
Hukumar Nukiliya ta duniya ta ce halin da ake ciki na da tayar da hankali.
Gwamnatin Rasha ta sanar cewa a yanzu haka yankin da babbar tashar nukiliya ta Ukraine take, kusa da birnin Zaporizhzhia na kudanci yana karkashin ikonta.
Gwamnatin ta sanar da hakan ne ga Hukumar da ke sa ido kan harkokin nukiliya ta duniya kamar yadda BBC ya ruwaito.
- Jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda sama da 200 a Neja
- MDD ta yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine
Hukumar nukiliyar, IAEA, ta ce Rashawan sun ba ta tabbacin cewa ma’aikatan Ukraine da ke aiki a tashar na ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Sai dai hukumar nukiliyar Ukraine ta ce tana tattaunawa da dukkanin tashoshinta na nukiliyar, kuma aiki na ci gaba da gudana a dukkanninsu.
Amma Darakta Janar na Hukumar Nukiliyar ta duniya, Rafael Grossi, ya shaida wa taron manema labarai cewa halin da ake ciki na da tayar da hankali.
Ya ce abu mafi muhimmanci a nan shi ne, idan ana rikici, lalle akwai fargabar kai hari, ko kuma ma a samu hadarin tashin makaman.
Tashar Zaporizhzhia tana dauke da shida daga cikin na’urorin nukiliya 15 na Ukraine.
Kafin yanzu dai hukumomin da ke kula da nukiliyar Ukraine sun bukaci taimakon hukumar nukiliya ta duniya, da ta taimaka ta tabbatar da tsaro a cibiyarta ta Chernobyl da ke arewacin Ukraine, wadda dakarun Rasha suka kwace.