Mun kwato N30bn a hannun Akanta-Janar —EFCC

Bawa ya ce EFCC EFCC za ta yi wa ’yan Najeriya gwanjon wasu rukunin gidaje da wasu dukiyoyi masu tarin yawa da hukumar ta kwato.

Mun kwato N30bn a hannun Akanta-Janar —EFCC

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta ce ta kwato kudi sama da Naira biliyan 30 daga cikin biliyan N109 da ake zargin tsohon Akanta-Janar na Kasa, Ahmed Idris, ya yi sama da fadi da su.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, ya ce kafin karshen shekara, hukumar za ta yi wa ’yan Najeriya gwanjon wasu rukunin gidaje da wasu dukiyoyi masu tarin yawa da hukumar ta kwato daga barayin dukiyar kasa.

Da yake bayani a ranar Alhamis, a taron mako-mako da suke yi kan ayyukan hukumar, shugaban na EFCC ya ce cikin tsarinsu na gano hada-hadar kudi, nan da shekara uku zai yi wuya a iya karkatar da dukiyar kasa zuwa wani asusun banki.

Bawa, ya yi karin haske kan ayyukan hukumar tare da irin fadi-tashin da take yi wajen yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.

Tun da farko dai, Akanta-Janar Ahmed Idris an zarge shi da yin sama da fadi da kudi biliyan 109 daga ofishin gwamnati.

Daga bisani EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu inda aka aike shi zuwa gidan yari.

Amma daga baya ya samu beli, wanda tun daga wancan lokaci ake ci gaba da shari’a kan almundahanar da ake zargin sa da aikatawa.

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya

’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu a Sakkwato

Gwamnati za ta mayar da yara 5,000 makaranta a Jigawa